Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya shawarci matasa su guji tada hankula da rikici yayin kamfen da zabe.
Sarkin ya yi wannan kirar ne yayin wani taro na musamman na addu’o’i da masarautarsa ta shirya ranar Asabar don bikin cikar Najeriya shekara 62 da samun yanci Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma yi kira ga yan siyasa da shugabanni su guji furta munanan kalamai da maganganu na kiyayya yayin kamfen.
Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya shawarci matasa su guji tada hankali da dabbancin siyasa a yayin da aka fara yakin neman zaben 2023, rahoton The Punch.
Sarkin ya bada wannan shawarar ne a ranar Asabar lokacin da ya jagoranci addu’a da masarautar ta shirya don murnar cika shekaru 62 da samun yancin Najeriya.
Kada ka bari komai ya wuce ka Ya gargadi matasan kada su yarda yan siyasa su yi amfani da su wurin cimma bukatun kansu ya yi kira gare su su guji tada hankula a jihar da kasa baki daya.
Sarkin ya ce: “Ina son amfani da wannan damar in yi kira ga matasa su guji daban siyasa da duk wani abin tada rikici yayin zabe.”
Sarkin ya kuma yi kira ga yan siyasa a kasar su kiyaye furta maganganu marasa kyau da maganganun kiyayya yayin yakin neman zabe.
An shirya taron addu’ar ne don rokon Allah game da zaben 2023 Ya ce an yanke shawarar shirya taron ne domin neman Allah ya saka a yi zabe lafiya a shekarar 2023.
Sarki Bayero ya ce: “An shirya taron ne don yi wa kasa addu’a a yayin da ta ke cika shekaru 62 da samun yanci da kuma yin zaben 2023 lafiya.”
Mambobin masarautar ta Kano da wasu masu fatan alheri daga sassa daban-daban na jihar ne suka halarci taron.
Sarkin Kano Ya Naɗa Sheikh Aminu Daurawa Matsayin Limamin Masallacin Jami’ar Skyline A wani rahoton, mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya naɗa babban malamin addinin Musuluncin nan, Assheikh Aminu Ibrahim Daurawa, a matsayin limamin sabon masallacin jami’ar Skyline.
Jami’ar Skyline na daya daga cikin jami’o’in kudi masu zaman kansu a jihar Kano.
Source:legithausang