Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sunusi II, ya gudanar da hawan Sallah, bayan jagorantar Sallar Idi a Masallacin Kofar Mata da ke Jihar Kano.
Ya jagoranci Sallar Idin ne a masallacin Juma’a na Kofar Mata da ke Jihar, sakamakon mamakon ruwan sama da aka tashi da shi, wanda ya hana gudanarwa a filin Idi.
Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusif, da sauran manyan jami’an gwamnatin Jihar sun yi Sallar idin ne tare da Sarki Sanusi.
Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da rundunar ‘yan msandan Jihar ta fitar da sanarwar haramta hawan Sallah a Jihar sakamakon rikicin masarautar da ake fama da shi.
Matakin da tuni gwamnatin jihar, ta ce hurumin gwamnan jihar ne, ya ayyana ko za a yi hawan sallah ko ba za a yi ba, kasancewarsa lamba daya a bangaren kula da harkokin tsaron jihar.
Shi ma dai Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya gudanar da Sallar Idin a karamar fadar Nassarawa kamar yadda ya sanar tun da farko.
A wani labarin na daban gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi alƙawarin bayar da cikakken goyon baya da tallafi ga iyalan ’yan Rundunar Kare Jama’a ta Zamfara (CPG) ‘Askarawan Zamafara’ da suka rasa rayukansu a yaƙin da ake yi da ’yan bindiga.
A ranar Alhamis ne aka gudanar da bikin karrama wasu jami’ai 20 na ‘Askarawan Zamfara’ da lambobin yabo bisa ƙwazon da suka nuna a lokacin gudanar sa ayyukan su. An gudanar da bikin ne a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa jami’an da aka ƙawata sun taka rawar gani sosai.
A cewar sanarwar, jami’an da aka yi wa adon suna ƙarƙashin jagorancin Birgediya Janar Lawal Bature Mohammed ne, Kwamandan Rundunar Kare Al’umma ta jiha.
“A ranar Alhamis, Gwamna Dauda Lawal ya yi wa jami’ai 20 waɗanda suka taka rawar gani wajen gudanar da ayyukansu ado da lambobin yabo. Dukkanin 20 ɗin sun kasance gwanaye a fagen yaƙi da ‘yan bindiga domin tabbatar da zaman lafiya a Jihar Zamfara.”
A yayin jawabin nasa, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada sadaukarwar gwamnatinsa wajen jin daɗin Askarawan Zamfara tare da yin alƙawarin bayar da cikakken goyon baya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.
“Ku yi la’akari da yi muku ado a matsayin wata hanya ta zaburar da ku don ƙara himma a cikin wannan muhimmiyar sadaukarwa da ku ke yi.
“Ba za mu iya biyan ku kan hidimar da ku ke yi wa ƙasa da bil’adama ba; Abin da kawai za mu iya yi shi ne ƙarfafawa don jin daɗin ku.
“Ina so in tabbatar muku da cewa muna da wani shiri da aka yi wa iyalan ’yan Rundunar Kare Jama’a da suka rasa rayukansu a bakin aiki. Za mu biya musu dukkan buƙatunsu da kuma ba su dukkan tallafin da ya dace.”
DUBA NAN: Zamewar Tinubu: Atiku Abubakar Yayiwa Shugaban Kasa Jaje
Tun da farko, Birgediya Janar Lawal Bature Mohammed, kwamandan Rundunar Kare Al’umma, ya bayyana cewa an zaɓo jami’ai 20 ne daga ƙananan hukumomi daban-daban na jihar bisa yadda suka nuna ƙwazo.