Mai shari’a Liman Mohammed na babbar kotun tarayya da ke Kano ya yanke hukunci a yau Alhamis cewa tana da hurumin sauraren ƙarar da Aminu Babba Dan Agundi ya shigar kan batun tsige Sarki Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano na 15 da gwamnatin jihar Kano ta yi.
Wannan hukuncin ya bai wa Sarki Aminu Ado damar kalubalantar halaccin tsige shi a kotu.
Wannan hukuncin ya biyo bayan umarnin da wata babbar kotun jihar Kano ta bayar na sauya tsige Sarki Aminu Ado da wasu sarakuna huɗu da aka tuɓe.
Hukuncin mai shari’a Mohammed ya tabbatar da cewa shari’ar Sarki Aminu za ta iya ci gaba da gudana, wanda ke nuna dambarwar shari’a kan shugabancin masarautar Kano bai ƙare ba.
Tun da farko dai babbar kotun tarayya ta bayar da umarnin wucin gadi na hana gwamnatin jihar Kano aiwatar da dokar masarautar jihar ta 2024, wanda ya kai ga tsige Sarki Aminu Ado.
Duk da tsige shi da kuma naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16 da Gwamna Abba Yusuf ya yi, Sarki Bayero na ci gaba da yin sha’anin mulki a matsayin Sarki, inda ya ci gaba da zama a wata ƙaramar fada da ke Nassarawa a ƙarƙashin umarnin kotu.
A wani labarin na daban ƴan kasuwa da dama a kan titin IBB, cikin birnin Kano, sun rufe kasuwancinsu ba zato ba tsammani, don bin abokan kasuwancinsu zanga-zangar adawa da sanarwar korar su a inda shagunansu suke.
Majiyoyi sun ce gwamnatin jihar na shirin rusa shaguna da rumfunan da ke yankin wanda hakan ya haifar da hargitsi yayin da ƴansanda suke sintiri a yankin suna harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa ƴan kasuwa da sauran jama’a.
A ranar Litinin ne hukumar tsare-tsare da raya birane ta jihar Kano, KNUPDA, ta ba ƴan kasuwar sa’o’i 48 da su bar yankin.
Shugaban ƙungiyar ƴan kasuwar, Yakubu Muhammad, ya ce hukumar KNUPDA ta bayar da sanarwar ne ga ƴan kasuwar da shagunansu ke kusa da wajen da aka rusa shekarar da ta gaba ta, kusa da filin Sallar Idi.
Malam Muhammad ya ce tun sama da shekaru 18 Majalisar Masarautar Kano, ta raba musu wurin bisa shawarar Marigayi Galadiman Kano Tijjani Hashim, inda daga baya gwamnati ta tsara yadda za a raba musu shaguna da rumfuna.
DUBA NAN: Matakan Da Gwamnatin Kano Ta Dauka Dangane Da Ilimi
Sai dai kawo yanzu gwamnatin jihar Kano ba ta ce uffan kan lamarin ba.