‘Yan uwan marigayiya Saratu Gidado Daso sun shaida wa manema labarai cewa mutuwar fuju’a ta riske ta a yau Talata, bayan ta kammala sahur ta kwanta bacci.
A wani dabarin daga kasashen ketare baya bayan nan, gwamnatin Amurka ta sanar da shirin ta na gudanar da bincike kan ababen hawa masu amfani da lantarki kirar kasar Sin da ake shigarwa kasar, bisa fakewa da batun tsaron kasa, yayin da a daya hannun ita ma kungiyar tarayyar Turai EU, ta fitar da wasu ka’idoji dake umartar bangaren jami’an kwastam, da ya rika yin rajistar irin wadannan ababen hawa kirar kasar Sin da ake shigarwa nahiyar.
Game da hakan, sassa masu ruwa da tsaki daga ma’aikatar raya masana’antu da fasahar sadarwar Sin, sun yi tsokaci da cewa, akwai wasu kasashe da yankuna, wadanda ba tare da wata kwakkwarar hujja ba, suna aiwatar da ka’idojin sanya shingen cinikayya ga ababen hawa masu amfani da lantarki kirar kasar Sin, wanda hakan ya sabawa dokokin cinikayyar kasa da kasa na kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kuma hakan zai yi matukar illata ayyukan masana’antu masu nasaba, da ma tsarin shigar da ababen hawa sassan duniya daban daban, tare da cutar da moriyar masu sayayyar hajojin. Bangaren na Sin ya tabbatar da cewa, wannan mataki zai kuma haifar da tafiyar hawainiya ga matakan wasu kasashe, na sauya akala zuwa amfani da makamashin lantarki a ababen hawa.
DUBA NAN: Gwamnan Kano Ya Bukaci EFCC Ta Cigaba Da Binciken Dala
Jami’an ma’aikatar, sun kara da cewa, a shekarun baya bayan nan, Sin na nacewa hanyar samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da rage fitar da iskar carbon mai dumama yanayi, da samar da ci gaba mai dorewa. Kana kasar na aiwatar da matakan yayata ci gaban fasahohi, da gina masana’antu masu bin tsarin kare muhallin halittu, da samarwa sassan kasa da kasa hajoji masu araha, nau’o’i daban daban, da ababen hawa masu amfani da sabbin makamashi, da kayayyakin sarrafawa, da sassan kayan gyara, da sauran abubuwan bukata a fannin. Hakan ya gabatarwa duniya da kwarewa ta zahiri, ya kuma samar da sabon mafari mai karfi a fannin raya amfani da sabbin makamashi a ababen hawa a duniya baki daya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)