Yan bindiga sun sace tsohon sakataren Hukumar Ƙwallon Kafa Ta Najeriya, NFF, Sani Toro, Premium Times ta rahoto.
An sace tsohon sakataren na NFF ne a hanyarsa ta komawa Bauchi daga Abuja inda ya hallarci daurin auren dan tsohon shugaban NFF Aminu Maigari.
Yan sanda sun yi martani kan lamarin Kakakin yan sandan Jihar Bauchi, Ahmed Wakil, ya tabbatar wa Premium Times sace shin, amma ya ce ba shi da cikakken bayanin tunda abin ba a Bauchi ya faru ba.
“Eh, labarin gaskiya ne. Na yi magana da ɗaya cikin yayansa, wanda ya fada min cewa an sace shi ni kusa da hanyar Akwanga a Nasarawa yayin da ya ke dawowa daga Abuja. Idan na samu karin bayani zan sanar da ku,” in ji Mr Wakil.
An rawaito cewa an sace Mr sani Toro ne tare da tsohon mataimakin kocin Super Eagles, Garba Yila. Kawo yanzu ba a san wanda suka sace shi ba kuma ba su riga sun tuntubi yan uwansa don neman kudin fansa ba.
Garkuwa da mutane don neman kudin fansa ya zama ruwan dare a wasu jihohin Najeriya kuma kungiyoyin yan bindiga daban-daban ke aikata abin. Dakaci karin bayani…
A wani labarin na daban hukumar zaben Najeriya INEC ta bayyana Abiodun Oyebanji, dan takarar jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar gwamnan jihar Ekiti da aka yi a jiya Asabar.
Bayan kammala kidaya kuri’un da aka kada, sakamakon ya nuna cewar, Oyebanji, wanda ya samu nasara a kananan hukumomi 15 daga cikin 16 na jihar Ekitin, ya samu kuri’u 187,057.
Segun Oni dan takarar jam’iyyar SPD ne ya zo na biyu da kuri’u 82,211, yayin da Bisi Kolawole na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 67,457.
‘Yan takara 16 ne suka fafata a zaben na ranar Asabar, inda aka kada jumillar kuri’u dubu 360,753, sai dai dubu 8,888 basu karbu ba.