Sanatoci a wanna satin sun fara tantance sabbin ministocin da shugaba muhammadu buhari ya nada.
Tantance ministocin dai anayin sa ne a farfajiyar majalisar dattawan Najeriya.
Tare da cewa ya rage gwamnatin Buhari kasa da shekara daya amma Buharin ya bukaci sanatoci da su tantance masa sabbin ministoci bakwai da yake son nadawa kuma su shiga cikin majalisar zartaswa ta Najeriya.
Minaitocin an nada su ne daga kudu maso gabas, sa’annan kuman zabo minista daya daya daga arewa maso gabas kudu maso yamma da kuma kudancin kudu.
Sunayen ministocin gasu kamar haka -Henry Ikechukwu – Abia State, Umana Okon Umana – Akwa-Ibom State, Ekuma Joseph – Ebonyi State, Goodluck Nana Obia – Imo State, Umar Ibrahim Yakub – Kano State, Ademola Adewole Adegorioye – Ondo State, and Odo Udi – Rivers State.
A wani labarin na daban biyo bayan maganganun tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, wani daga cikin dattawan arewa mazaunin kano Dr. Bature Abdulazzeez mon ya bayyana bayanan obasanjon a matsayin abin takaici inda ya bayana obasanjon a matsayin maci amana.
Dr. Abdulzazeez wanda yake magana da gidan jaridar Vanguard a ranar laraba ya bayyana jawaban Obasanjo a matsayin tsananin nuna kiyayya gami da tsana ga arewa amma Obasanjon ya fake a bayan Atiku Abubakar, tare da cewa a cewar Abdulazeez Obasanjon ya samu darewa kujerar shugabancin Najeriya ne gudummawar ‘yan arewa.
Bature ya bayyana cewa kiyayyar Obasanjo ce ta kori mutane daga wajen sa lokacin yana kan kujerar mulki ba Atiku ba amma yanzu yana dora laifin hakan a kan Atiku Abubakar tare da cewa zabe yana gabatowa.
”Dangane da abinda Obasanjon ya fada dangane da Atiku koda mutum ba dan siyasa bane kishi zai sanya shi ya fito ya kare atikun a cewar Bature”
Shi dai tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a wata fira da ‘yan jaridu ya bayyana zaban Atiku matsayin mataimakin sa a shekarar 1999 a matsayin kuskure ne.