Fitaccen sanata daga jihar Neja ya tsallake rijiya da baya yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki gidan sa.
Rahoton da muka tattaro ya bayyana cewa, an kai farmaki gidan sanata ne tare da tsammanin yana gida alhalin ya koma Abuja.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai ‘yan sanda basu yi bayani game da faruwar lamarin ba.
Sanata mai wakiltar mazabar Neja ta Gabas a majalisar dattawa, Alhaji Muhammad Sani Musa ya tsallake rijiya da baya a wani kazamin hari da aka kai gidansa da niyyar sheke shi a birnin Minna.
‘Yan bindigan sun farmaki gidan sanatan ne tare da tsammanin yana gida bayan dawowarsa daga Abuja zuwa gidansa da ke kusa da asibitin Alheri da ke yankin Tunga a Minna, babban birnin jihar.
Sai dai, cikin rashin sani, sanatan ya koma Abuja a yammacin ranar kafin ‘yan ta’addan su farmaki gidansa da dare, Daily Sun ta ruwaito.
Duk da cewa hukumar ‘yan sanda bata tabbatar da faruwar labarin ba ya zuwa yanzu, an ce tsagerun da suka zo gidan sanatan ne tare da wasu mutum da ke sanya da kakin ‘yan sanda da na soji da misalin karfe 8 na dare.
An ruwaito cewa, mutane biyu da ke sanye da kakin sojin sun tsaya domin sanya ido a bakin kofa, yayin da wasu hudu suka shiga gidan sanya da kayan gida.
Sun shiga gidan ne bayan da suka shaidawa ‘yan sandan da ke gadi cewa sun zo bincike ne daga ofishin mai shugaban kasa shawari kan harkokin tsaro.
A cewar majiyar kusa da gidan sanatan, ‘yan ta’addan sun shaidawa ‘yan sandan cewa, sun samu labarin an ajiye makamai da alburusai har ma da tain kudaden waje a cikin gidan sanatan.
Tuni ‘yan snadan suka gano abin da suke kitsawa, inda aka yi sa’ar kai bayani ga wani abokin sanatan, wanda mashawarci ne ga gwamna Sani Bello na jihar, Alhaji Nma Kolo cewa ga wasu ‘yan bindiga sun farmaki gidan abokinsa sanata.
Bayan samun labari, mashawarcin gwamnan ya sanar da dan takarar gwamnan APPC na jihar, Alhaji Umar Bago, wanda tuni ya duro gidan don ganin abin da ke faruwa.
An kuma tattaro cewa, ‘yan bindigan sun kama dakin otal kafin nufin aiwatar da barnar da suka shirya a gidan sanatan, kuma har ya zuwa yanzu ba a gano su wanene ba.
Wannan ne karo na biyu da ake kokarin farmakar sanatan, inda a farko aka yi kokarin hallaka shi a gidansa da ke Minna shekaru biyu da suka gabata a salo mai kama da wannan, amma ba a same shi ba.
Ba a samu tattaunawa ta wayar harho da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ba, DSP Wasiu Abiodun, amma ya yi sakon tes cewa zai ba da bayani daga baya.
Sai dai, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Mr Emmanuel Umar ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce ‘yan sanda na kan bincike game da lamarin.
Kana ya bukaci jama’ar gari da su kwantar da hankali, inda yace nan ba da dadewa ba za a samu cikakkun bayanai kan yadda lamarin ya faru.