Sanata shehu sani wanda yana daya daga cikin wadanda muryar su tayi amon gaske a bangaren rajin kare hakkin dan adam, yayi magana dangane da yadda ake gudanar da shari’ar shugaban kungiyar ‘yan aware ta kabilar ibo zallah wacce ta shahara da IPOB a takaice kuma take fafutukar ballewa daga tarayyar najeriya gami da kafa kasar kabilar ibo zallah.
Sanata shehu sani kamar yadda ya bayyana a shafin sa na tuwita ya tabbatar da cewa ya kamata gwamnatin najeriya ta sani cewa yanzu fa muna karni na ashirin da daya ne kuma duniya ta waye an wuce lokacin da wata gwamnati zata dinga jan mutane a bai bai ba tareb da suna sanin halin da ake ciki ba.
Lamarin kanu ya shafi ‘yan najeriya kai tsaye saboda hakanan suna da hakkin su san halin da ake ciki kai tsaye kamar yadda sanata shehu sani ya tabbatar a shafin sa na tuwita.
A yau litinin wanda yayi dai dai da 26 ga watan yuli ne dai ake gudanar da shari’ar shugaban na kungiyar ‘yan awaren ibo, kuma tuni ya bayyana a kotun dake abuja sanye da shigar yahudawa, abinda ake ganin kamar ya zama wani salo na nuna alaka da haramtacciyar kasar isra’ila.
Ana zargin kanu da cin amanar kasa gami da gujewa shari’a anda wadannan laifukan manyan laifuka ne a kundin tsarin mul;kin najeriya amma sai dai magoya bayan kanu daga bangaren kabilun ibo sun karyata wannan zargi kuma sun zargi gwamnatin najeriya karkashin shugaba muhammadu buhari da laifin sato shugaban na IPOB daga kasar da ya gudu.
Koma dai menene ana sa ran a cigaba da gabatar da shari’ar da kanu ya gujewa a wancan lokaci bayan ya karbi beli.
Babban abin tsoro shine kada jinginuwar kanu da haramtacciyar kasar isra’ila kamar yadda yazo kotu da shigar yahudawa ya sanya gwamnatin haramtacciyar kasar isra’ilan tayi kokarin katsalandan a harkokin ccikin gidan najeriya.