Sojojin Nigeria ne sukai lugudan wuta akan sansanin ‘yan kungiyar jihadi ta boko haram guda biyu dake sambisa kuma sukai musu mumunar illa.
Harin wanda sharin aiwatar da zaman lafiya na sojin mai suna “Operation Hadin Kai” ya kai ta jirgin saman yakin sojojin sama ne ya bada wannan nasarar.
Sojoji na kirga nasarar da suke samu a yaki da Boko Haram, amma a jihar Zamfara sojojin ne suka rasa ransu a wani hari da ‘yan bindiga suka kai musu.
Sama da ‘yan Boko Haram 150 ne suka rasa ransu a wani hari da sojijin saman Nigeria sukai kaiwa’yan kungiyar a dajin sambisa.
Kamar yadda wasu rahotanni suka tabbatar jirgin saman sojin Nigeria ya kai hari a ranar 21 ga watan Disambar wannan shekarar a wani sansanin ‘yan Boko Haram da ke Matari a karamar hukumar Bama ta jihar Barno.
Wata majiya a hukumar tsaron soji ta fadawa jaridar Zagazola cewa harin yayi mumunar illa ga maboyar ‘yan taddan da suke a yankin tafkin ChadZagazola.
Majiyar tace manyan kwamandojin kungiyar da suka hada da Babba Tukur, A kahid na cikin wanda suka rasa ransu ab harin a sansanin Mantari da kuma na sansanin su na Maimusari.
Majiyar tace da ta samu wani kishin-kishin din kai harin ne bayan da ‘yan ta’addan suka gana da yan uwansu da suke zaune a Mantari, daga bisa ni suka karbi makamai da man mota suka koma.
Su kuma sojojin sukai amfani da damar suka kai musu hari.
Yan Boko Haram Sun Rasa Manyan Kwamnadoji Yan Boko Haram sun yi asarar mayaka da dama, wanda daga cikinsu akwai Abu Isa, Khaid, Ali Ghana Kaid da kuma wasu manyan mayakan daga yankin Gaizuwa.
Tun da fari dai an tabbatar da ba’a samu asarar rayukan yan kungiyar ba, sai dai rauni da ciwuka, amma daga bisani an ambato yawan mayakan da suka rasa ran nasu.
Majiyar tace mayakan sun sun taru ne a wani budeden waje wanda yake da tazarar mita 500 da garin Mantari, kuma an tabbatar da ba kowa a kusa da wajen sannan aka kai harin.
Hare-haren dai kungiyar Boko Haram yai sauki a ytankin tafkin Chad.
Source:LegitHausa