Sama da yara dubu 1 ne aka sace a daga makarantun Najeriya a wannan shekarar, a cewar Save the Children, wata kungiya mai zaman kanta.
Kungiyar ta ce ta’azzarar da satar yara ‘yan makaranta ta yi a tsakanin shekarar 2020 da 2021 ne ma ta tilasta rufe makarantu, lamarin da ya jefa tsarin ilimin kasar cikin hatsari, sama da yadda ake tsammani.
Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce daga watan Janairu zuwa Agustan shekarar 2021, sama da yara dubu 1 ne aka yi garkuwa da su, inda da dama daga cikinsu ke hannun masu garkuwar har yanzu.
Babban bankin Najeriya ya musanta ikirarin da ake cewa ya umurci bankuna su mayar da asusun ajiyar abokan huldarsu na kudaden kasasehn waje zuwa na Naira.
Bankin ya sake yin tuni da cewa ya sha bada tabbacin cewa babu wani shirn mayar da asusun ajiyar kudaden kasashen waje zuwa na Naira, don kawai yana so ya magance karancin dalar Amurka.
Daga nan sai banki ya ja kunnen kamfanoni da daidaikun mutane a game da amfani da hatimi ko alamar bankin, yana mai cewa ya sanar da hukumomi, kuma duk wanda aka kama zai dandana kudarsa.