Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi, ya amince da biyan albashin watan Afrilu daga Juma’ar nan domin saukaka wa al’umma shagulan bikin karamar sallah cikin annashuwa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun mukaddashin shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Safiyanu Garba Bena kuma aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi.
A cewar sanarwar, irin wannan alherin da gwamnatin jihar Kebbi ta yi, a karkashin jagorancin Sanata Abubakar Atiku Bagudu, na bai wa ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho na jihar damar gudanar da bukukuwan Sallah cikin sauki.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, tuni bankunan daban-daban suka fara fitar da sanarwar albashi ga ma’aikata bisa ga umarnin da Gwamna ya bayar na daukar matakin gaggawa.