Rahoto ya bayyana cewa, ‘yan bindiga sun hallaka wasu mutane uku a wani yankin jihar Sakkwato.
Sun kuma yi awon gaba da dukiyoyin al’umma tare da fatattakar kauytuka takwas a yankin.
Wani shugaba a yankin ya bayyana yadda lamarin ya faru, tare da bukatar a kawo musu dauki Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe mutane uku a kauyen Garin Zogo da ke karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sakkwato.
Sun kuma fatattaki kauyuka takwas a karamar hukumar, Daily Trust ta ruwaito. Da yake tabbatar da hare-haren, Kansilan da ke wakiltar yankunan, Ibrahim Muhammad Saraki ya ce an kaiwa Garin Zogo hari ne a ranar Juma’a da misalin karfe 10:30 na dare.
“Sun kashe mutane uku sannan suka ji wa daya rauni. Sun kuma yi awon gaba da dabbobi, sun kutsa cikin shaguna da yawa sun kwashe kayan da ba a san adadinsu ba,” inji shi
A cewarsa, ‘yan bindigan sun kuma kai hari kauyukan Nasarawa, Gidan Idi da Rambadawa a ranar Asabar inda suka raunata mutum uku tare da sace dabbobi.
Ya kara da cewa, ‘yan bindigan sun kara shiga gidajen mazauna yankin tare da kwace musu kayayyakinsu.
“Ba ma zama cikin kwanciyar hankali a cikin garuruwanmu saboda kisan da ke faruwa a kowace rana. ”Kamar yadda nake magana da kai yanzu mutanenmu ba su kwana a gidajensu. Suna kwana a garin Sabon Birni sannan suna dawowa da safe, har da ni. ”
”Kuma akwai wasu kauyukan da ba kowa ciki kamar Rambadawa, Garin Idi, Tudun Wada, Nasarawa, Tamindawa, Garin Ango, Tsaunar Dogo da Tashalawa,” in ji shi
Hakazalika ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta kawo musu dauki. Mashawarci na musamman ga Kansilan kan harkokin tsaro, Lamiru Umar yayin da yake tabbatar da hakan ya ce, a yanzu haka wasu mutanensu na samun mafaka a kauyen Tsululu da ke Jamhuriyar Nijar.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na Sakkwato, ASP Sunusi Abubakar ba a samu jin ta bakinsa ba.
A wani labarin, Wasu ‘yan bindiga da sanyin safiyar ranar Lahadi sun mamaye yankin Kuchiko a karamar hukumar Bwari da ke Babban Birnin Tarayya (FCT) inda suka yi awon gaba da wani mazauni da dansa.
Daily Trust ta tattaro cewa ’yan bindigan wadanda yawansu ya kai ashirin sun afka wa yankin, wanda aka fi sani da El-Rufa’i Estate, da karfe 12 na dare kuma suka fara harbi ba kakkautawa.
Bayan sun fi karfin jami’an tsaro, ‘yan bindigan, sun yi amfani da wukake da adduna, suka nufi gidan wanda aka sacen suka yi garkuwa da shi da dan nasa.