A cigaban da amsar sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 daga kananan hukumomin jihar Bauchi, zuwa yanzu Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP shi ke kan gaba da rinjaye mai gwabi kan sauran abokan hamayyarsa.
WARJI LGA:
APC 11,862
PDP 17,732
NNPP 424
LP 185
Bogoro LGA:
APC 4,850
LP 6,866
NNPP 798
PDP 15,156
Dass LGA:
APC 10,939
LP 705
NNPP 397
PDP 13,242
Jama’are LGA:
APC 8,410
LP 22
NNPP 3,638
PDP 12,535
Dambam LGA:
APC 7,588
LP 42
NNPP 2,586
PDP 12,203
GIADE LGA
PDP 11,977
APC 10,382
NNPP 4002
LP 17
DARAZO LGA
APC 16,070
PDP 17,459
NNPP 1,895
Kananan Hukumomin bakwai aka yi a cikin 20 zuwa yanzu.
Kawo yanzu PDP ke rinjaye a jihar Bauchi
A wani labarin na daban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta dage zamanta na tattara sakamakon zabe daga jihohi zuwa gobe Litinin 27 ga Fabrairu, 2023 da misalin karfe 11 na safe.
Ku tuna cewa, Cibiyar tattara sakamakon an bude ta a hukumance ne da misalin karfe 1 na ranar Lahadi sannan aka tafi hutu zuwa karfe 6 na yamma bayan an zauna kasa da mintuna 30 sabida babu wani sakamakon zaben shugaban kasa daga jihohi 36 na tarayya da babban birnin tarayya Abuja.
Shugaban zabe, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ci gaba da zama da misalin karfe 6 na yammacin ranar Lahadi, ya kira jami’in zabe na jihar Ekiti, Farfesa Akeem Lasisi, wanda ya shirya don gabatar da sakamakon zabe kamar haka:
Farfesa Lasisi ya gabatar da sakamakon kamar haka:
APC – 201,494
LP – 11,397
NNPP – 264
PDP – 89,554
Yawan kuri’un da aka kada – 314,472
Source:LeadershipHausa