Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka CAF, Patrice Motsepe, ya ce gasar cin kofin kasashen nahiyar ta AFCON za ta gudana kamar yadda aka tsara a kasar Kamaru, daga ranar 9 ga watan Janairu.
Wani karin dalilin da ke neman zama barazana ga gudanar gasar kofin na kasashen Afirka, shi ne batun yaduwar annobar Korona, cutar da ke neman sake barkewa a wani sabon zango, tun bayan gano sabon nau’inta mai suna Omicron da kwararru suka yi ittifakin ya zarce sauran nau’ikan annobar saurin yaduwa.
Wannan na zuwa ne bayan shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA Gianni Infantino, ya bayyana cewa tawagarsa na tattaunawa da Hukumar Kwallon Kafar Afirka CAF da kuma sauran masu ruwa da tsaki wajen shirya gasar cin kofin Afrikar a shekarar 2021, domin ganin ko za a iya dage gasar zuwa watan Satumba.