Dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar APC, Air Marshal Sadique Baba Abubakar (Mai ritaya) ya sha alwashin cewa, muddin ya zama gwamnan Jihar Bauchi, zai yi kokarin samar da sana’ar dogaro da kai ga mata da matasa ta hanyoyin da suka dace amma shi ba zai tsaya raba Akuyoyi a matsayin sana’ar dogaro da kai ba.
Sadique Abubakar ya kuma bayyana cewa, zai samar da cibiyoyin koyar da sana’ar hannu ga mata da matasan da za su iya tsayuwa da kafafunsu.
Sadique ya shaida hakan ne a ranar Alhamis ya yi kaddamar da takararsa ta Gwamnan Jihar Bauchi a jam’iyyar APC da aka gudanar a filin wasa na tunawa da Sa Abubakar Tafawa Balewa.
Gangamin taron ya samu halartar Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, Ministoci, jiga-jigan ‘yan siyasa da tawagar jagororin jam’iyyar na kasa.
Tsohon gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda da mataimakinsa Sagir Aminu Sale da wasu jiga-jigai da ‘yan takarar kujerar sanatoci da ‘Yan Majalisar tarayya na cikin mahalarta taron.
A wani labarin na daban babban limamin masallacin Abuja, Farfesa Ibrahim Ahmad Makari ya bayyana cewa yana nan kan ra’ayinsa bai yarda malami ya shiga siyasa ba, amma yana so a bambanta abubuwa guda biyu.
“Bana sha’awar malami ya shiga siyasa daban, amma idan ya kasance wannan malamin yana da wasu ilimi na rayuwa wanda ya shahara a kai, idan har ya shiga siyasa to ko ya yi kuskure ba za a danganta wannan kuskuren da addini ba. Abin da ake nufi dai ilimi ne kadai abin da ake bukata.”
Farfesa Makari ya kara da cewa akwai hakkin shugaba a kan talakawa, haka kuma akwai hakkin talakawa a kan shugaba wanda suka hada da biyyaya da kuma adalci.
Ya ce wannan zabe da za a gudanar shaida ce da Allah zai taimaya a kai ranar Lahira. Ya ce duk wanda ka zaba kar ka dauka abin wasa, kamar yadda ake raba wa mutane kudi ko omo domin su zabi mutum.
A cewarsa, wannan kudi ko omo da aka ba ka domin yin zabe, ka tabbatar da cewa shaida ce wanda Allah zai tambaye ka a ranar tashin kiya.
Farfasa Makari ya shawarci mutane su duba wadanda suka fi yi musu zaton alkairi kamar yin adalci, tausaya wa al’umma, to ka gina zabenka a kan wannan turbali na zaben shugaba.
Ya ce lallai mutane su duba wanda zai fi yi wa al’umma abubuwan da suka kamata a zaben shugaba domin su, sai ka yi kokarin gina zabenka a kan wannan ma’auni, amma duk lokacin da al’umma suka makantar da idanuwansu da hankulan su suka gina zabensu kan yadda mutane ke dibar miliyoyin kudade suna wazawa domin a zabesu har su hau wasu mukamai a kan su magance matsaloli, to lallai ba a shirya ganin lokacin magance matsalilin ba.
Ya ce ba zai taba iya fahimtar kishin kasa da za ta sa mutum ya dunga kwaso kudi yana kokarin sayan kujerar da zai yi wa al’umma aiki a kanta ba.
“Ni dai a fahimtata na kasa gane wannan kishin kasa wanda mutum zai kwaso kudi yana rabawa domin ya sayi kujerar da zai yi wa al’umma aiki a kanta.”
Farfasa Makari ya ce, “Akwai kalubale mai girma a gabanmu, abun da ake fadi na cewa ko ka zaba ko baka zaba ba za a zaben maka, wannan magana ba gaskiya ba ce.
Lallai wanda zai shugabanci al’umma, yanke hukunci na karshe yana hannun al’umma ne wanda suka bi layi domin zaban wanda zai shugabance su.
“Kaurace wa zabe, mutum ya ce ba zai yi zabe ba saboda wasu dalilai, to zai iya zama kara taimakon masu barna a kan barnar.
Saboda ko ka yi zabe ko ba ka yi ba a ranar da za a rantsar da shugaba dole ne a rantsar da shi.
Domin rashin zaben ka ba zai sa a kasa rantar da wanda za a rantsar ba.
“Saboda haka, ‘yan’uwa mu yi kokari mu zabi cancanta. Ka da mu mayar da kanmu koma-bayan da wani ya ce mana ku zabi wane, domin muna da hankular kanmu.
Sannan kar mu gina zabenmu a kan jam’iyya, dama a farkon maganana na fadi cewa damokuradiyyar nan iya kokarinta take yi ta yi abin da yake daidai, amma karka dauka komi nata daidai ne.
“Idan mutum ya ce maka jam’iyya kaza za ka zaba daga sama har kasa domin ra’ayinsa wanda ba ita ce daidai ba, kai kuma ka duba cancata.
Ya kamata mu gane babu wata jam’iyya a yanzu, domin ‘yan takara nawa ne suka sauya sheka wanda har wurin kamfen suna kuskuran iya fadin jam’iyyarsu, saboda sabawa wanda ya kasance jiya suke can, yanzu kuma suna nan, wanda hakan ne ya sa suke kuskuren fadin sunan jam’iyyunsu.
“Bai kamata ana ci gaba da yawo da hankalinmu ba, ya kamata mu yi kokarin gina zabenmu a kan wadanda suka cancanta,” in ji Farfasa Makari.
Source:Leadership