Sace ɗaliban Zamfara abin kunya ne – Amnesty
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’Adam ta duniya ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da harin da ƴan bindiga suka kai jihar Zamfara inda suka sace ɗaliban Jami’ar Tarayya ta Gusau.
Darektan ƙungiyar a Najeriya Mallam Isa Sanusi a tattaunawarsa da BBC ya ce yadda ƴan bindiga ke jefa rayukan mutane cikin haɗari haka babban abin takaici ne da kuma ƙyama.
Ya ce ya kamata gwamnatin Najeriya da dukkanin hukumomin da nauyi ya rataya a wuyansu su tashi tsaye domin kawo ƙarshen wannan ta’asa da cin karen da ƴan bindigar ke yi babu babbaka.
Darektan ya ce, “wannan abin ya isa haka mutanen jihar Zamfara tura yanzu ta kai bango ya kamata a ceto su daga hannun waɗannan mutane waɗanda suke cutar da su suna kashe su sun hana su noma suna yi wa matansu fyaɗe suna yi wa ƴaƴansu fyaɗe yanzu kuma ga shi har suna hana yara makaranta.”
Gwamnati ta sha alwashin ceto ɗaliban
Yayin da ƙungiyar Amnesty ke wannan kira gwamnatin jihar ta Zamfara ta ce za ta yi duk abin da za ta iya da ɗaukar matakan ganin ta kuɓutar da ɗaliban mata, bayan guda shida da aka ceto.
Sace ɗaliban mata dai na ci gaba da ɗaukar hankalin jama’a da ƙungiyoyi a ciki da wajen Najeriya musamman ganin cewa wannan ba shi ne karon farko da hakan ke faruwa a ƙasar wadda ke fama da ƙalubalen tsaro.
Har zuwa safiyar Asabar ɗin nan gamayyar jami’an tsaro, wadda ta ƙunshi sojojin ƙasa da na sama da kuma ‘yan sanda, tana can tana ta fafutuaka, don ganin an ƙwato ɗaliban, kamar yadda Sulaiman Bala Idris, kakakin gwamnan jihar ta Zamfara ya gaya wa BBC.
Ya ce, gwamnatin jihar ta umarci jami’an tsro su tsaurara matakai a duk wani waje a jihar domin ganin ƴan bindigar ba su sulale da ɗaliban ba ba su kuma samu damar aikata wata ta’asa a jihar ba.
Ya ce da aukuwar lamarin jami’an tsaro sun yi nasarar ceto shida daga cikin ɗaliban kuma sun hallaka da dama daga cikin ƴan bindigar, yayin da suke ci gaba da ƙoƙarin kuɓutar da sauran.
Kakakin na gwamnan Zamfara ya ce, “abin mamakin shi ne waɗannan ƴan bindiga shigowa suka yi daga wata jiha sun zo ne domin su yi wannan ta’addanci na satar waɗannan ɗalibai, amma in shaa Allahu daga rahotannin da muke samu daga jami’an tsaro da suke binsu cikin dazuka ba za su iya fita da waɗannan ɗalibai ba daga cikin Zamfara.”
Ya ƙara da cewa, “da yardar Allah za a ƙwato ragowar ɗaliban da suka rage a hannun ƴan bindigar kuma za a kiyaye aukuwar hakan nan gaba.”
Da sanyin safiyar Juma’a ne ƴan bindigan suka sace ɗaliban mata daga gidaje uku na kwanansu, a ƙauyen Sabon Gida da ke yankin ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar Zamfarar.
A hukumance dai har yanzu ba a kai ga tantance adadin waɗanda abin ya rutsa da su ba.
Aukuwar wannan lamari dai, wani lamari ne game da ke nuna yadda matsalar sace-sacen jama’a don neman kuɗin fansa, ke ta yin ƙamari a yankin arewa maso yammacin Najeriya.