Ana ci gaba diga ayar tambaya tun bayan gudanar da babban taron manema labarai a makon jiya wanda Kwamitin Dattawan Jam’iyyar APC, reshen jihar Filato ta Najeriya ya shirya don bita kan sha’anin tsaro da kuma sabuwar matsalar data kunno kai wacce take da alaka da lamarin na tsaro.
A yayin gudanar da taron a ranar 3 ga watan Satumba, kwamitin ya bukaci Gwamnan jihar Simon Lalong da ya sake nazartar badalakar daukar wasu matasa aikin soji da tsohon Gwamnan jihar Jonah Jang ya yi tare da tura su Isra’ila domin samun horo.
A zamanin mulkinsa, an rawaito cewa, Jang ya dibi matasa 300 tare da tura su Isra’ila don ba su horo kan tsaro, amma tun bayan dawowarsu, har yanzu ba a ji duriyarsu ba.
Bayanai sun ce, akasarin matasan ‘yan kabilar Birom ne, wato kabilar tsohon Gwamnan, kuma an yi zargin cewa, ya dibe su ne domin cimma wata manufa ta murkushe abokan gaba a jihar amma ba don masalahar al’umma ba.
Jang ya mulki jihar Filato a tsakanin shekara ta 2007 zuwa 2015, yayin da a zamaninsa aka samu asarar dubban rayukan jama’a da kuma salwantar kadarori na biliyoyi a rikice-rikicen kabilanci.
Tsohuwar gwamnatin Jang ta PDP ta hakikance cewa, domin tabbatar da tsaro a jihar ta samar da sabuwar rundunar matasan a wancan lokaci.
Yanzu haka kwamitin dattawan APC ya bukaci Gwamna mai ci da ya lalubo wadannan matasa domin amfani da su wajen samar da tsaro a jihar, lamarin da ya zafafa muhawara kan lamarin.
Wannan muharawa dai, ta tayar da sabuwar kura a jihar ta Filato.
An dai gudanar da taron manema labaran ne ganin yadda lamurran tsaro suka kara sukurkucewa a baya-bayan nan jihar ta Fliato.
Bincike dai ya tabbatar dacewa ba yau ne aka fara samun matsalolin tsaro a jihar ta filato ba domin ko a shekarun baya ma an sha samun wasu bata gari suna kashe musulmi a jihar.