Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shetima ya kaddamar da sabuwar hukumar ayyukan hajji ta kasa (NAHCON) inda ya bukaci hukumar da su bullo da sabbin abubuwa a harkokin aikin hajjin Najeriya.
Da yake kaddamar da hukumar a fadar shugaban kasa mataimakin shugaban kasan a wata sanarwa da mai magana da yawun sa Stanley Nkwocha ya fitar, ya bukaci sabbin mambobin hukumar da su hada kai tare da kawo sabbin ra’ayi a ayyukan hukumar.
Shetima ya bayyana cewa, yin aiki a hukumar aikin hajji na da muhimmanci duba da cewa aikin hajji na cikin rukunnan Musulunci guda biyar.
Yace, fiye da aikin gwamnati wannan wani aiki ne wanda idan kuka hidimtawa alhazai Allah zai biya ku saboda haka aiki ne mai riba biyu, don haka wannan aiki ne na addini kafin ya zama aikin gudanarwa, a cewar mataimakin shugaban kasa.
Dangane da kafa sabuwar hukumar da kuma ayyukan dake gaban su, Shetima ya bayyana cewa ana sane aka zabo masu al’adu mabambanta kuma wadanda basu da gurbatattun abubuwa da suka faru a baya domin kawo sabbin ayyuka a hukumar aikin hajji ta Najeriya.
Kamar yadda aka saba zaku fuskanci Ƙalubale da dama amma ina rokon ku da ku hada karfi da karfe domin cimma nasara kan abinda aka sa a gaba.
Zan roke ku da ku sanya rigar tunani kuma ku fito da sabbin hanyoyi da zaku gamsar da alhazan Najeriya.
Duba Nan: Falasdinawa 30 Sun Rasa Rayukan Su A Wani Harin Isra’ila
Aiki ne mai wuyar gaske amma zanso ku dauka a zuciyar ku kuna bautawa Allah ne da wannan aiki, kamar yadda mataimakin shugaban kasan ya bayyana.