Yan Najeriya sun tsiri wani sabon salon kalubale a kafar sada zumunta don gwada ingancin sabbin Naira da aka buga.
Wannan na zuwa ne bayan da wani bidiyo ya yadu na yadda sabon kudin ke zuba yayin da aka tsoma su a ruwa.
Mutane da yawa sun yi martani ta hanyar yada bidiyon yadda nasu kudin ya kasance; yana zubewa ko a’a
Biyo bayan wani bidiyon da wata mata Chinazo a kafar Twitter ta yada, inda tace kudin Najeriya sun wanke tas bayan jikewa a ruwa, ‘yan kasar da dama sun yi sabbin bidiyo sun yada a intanet.
A bidiyon da ta yada, ta ce ‘yar uwarta ta wanke gudan N500 a aljihi cikin rashin sani, wannan yasa sabon kudin ya sauya zuwa farar takarda.
Wannan lamari dai ya dauki dumi a kafar Twitter, domin kuwa mutane da yawa sun shiga mamakin yadda kudi zan kasance haka.
A bangare guda, ‘yan kasar da dama na tambayar inganci da gaskiyar abin da matar ta yada a Twitter.
Ikrarin da Chinazo ya kawo wani sabon salo a kafar sanda zumunta, mutane suka fara jikawa tare da wanke sabbin kudin ganin ko da gaske suna zuba.
Sai dai, Dr Joe Aba, wata daraktar kasa a jami’ar DAI. DAIMaastricht ya yi tsokaci tare da wani gwaji a martani ga bidiyin Chinazo.
A cewar @DrJoeAbah, tabbas zubewar sabbin kudin Naira ba gaskiya bane, sai dai idan akwai wani lauje a cikin nadi.
A cewarsa:
“Na goga sabuwar N500 da ruwa da kuma auduga.
A’a, launin bai wanke ba.
Watakila matsalar a jikin gudan sabuwar N1,000 ne, wanda ni ban gwada ba.
Sabuwar N500 dai a wuri na bata wata matsala. Zan gwada a injin wanki sannan na ba ku rahoto daga baya.”
Har ila yau, @__bellefille ta karyata labarin cewa da gaske sabbin kudin Najeriya na zubewa idan suka jike.
Ta yada sabon bidiyo tare da cewa:
“Ga mutanen da ke cewa wai sabbin kudade na zubewa, meye-meye-meye.”
A tun farko, Chinazo ta ce ‘yar uwarta ce ta wanke N500 cikin kuskure, hakan ya maida sabon kudin zuwa farar takarda tas.