Sabon rikici ya kunno kai a jam’iyyar PDP reshen Kano
Wutar rikici ta ƙara ruruwa a PDPn jihar Kano duk da hukuncin kotu na baya-bayan nan da kuma matakin ɗaukaka ƙara daga ɗaya banagaren.
Lamarin ya faru ne bayan ɓangen Sadiq Wali wanda wata kotun tarayya ta ce ba shi ne ɗan takarar gwamnan ba, kuma ya ɗaukaka ƙara, daga baya ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓensa a jihar.
Sai dai ɓangaren da kotu ta ce shi halastacce na Muhammad Abacha ya fito ya yi Alla-wadai da wannan mataki yana cewa nuna raini ne ga kotu.
Bayanan da BBC ta samu na cewa a wannan Litinin ɗin ne ake sa ran kwamitin yaƙin neman zaben da ɓangaren Sadiq Wali suka ƙaddamar zai fara zama domin tattauna yadda zai gudanar da aikinsa.
A makon jiya ne aka kafa kwamitin, al’amarin da ya ƙara tayar da kura.
Ɓangaren Muhammad Abacha sun ce ba su tare da wannan matakin kamar, yadda Barrister Ibrahim Isa Wangida, lauyan jam’iyyar PDP a Kano ya shaida wa BBC.
To sai dai bangaren Sadiq Wali wanda ya ƙaddamar da kwamtin ya ce, waɗanda suke sukar wannan matakin ba su fahimci yadda tsarin yake ba, a ta-bakin kakinsu Dakta Yusuf Bello Danbatta.
Masharhanta dai na ganin duk wannan rikici da taƙaddama, jam’iyyar ce ke yi wa kanta sakiyar da babu ruwa, dai-dai lokacin da hankulan sauran jam’iyyu suka karkata ga yaƙin neman zaɓe.
Jam’iyyar ta PDP da ke sahun manyan masu hamayya a Kano har yanzu kanta a rarrabe yake lamarin da ake ganin hakan ba zai yi mata kyau, kasa da wata biyu a gudanar da zabe.