Jaridar LEADERSHIP Hausa ta rasa shugaban sashen fassara, Malam Sabo Ahmed Kafin-Maiyaki wanda ya rasu a ranar Alhamis 18 ga watan Mayu, 2023 yana da shekaru 54 a duniya bayan doguwar jinya.
A cewar sanarwar da iyalansa suka fitar, Malam Sabo ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya 10 da kuma dan uwa guda daya
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, za a yi jana’izarsa a ranar Juma’a, 19 ga watan Mayu, 2023 a Samaru, Zariya, a Jihar Kaduna.
Da yake karin haske, editan LEADERSHIP Hausa, Abdulrazaq Yahuza Jere, ya bayyana Malam Sabo a matsayin babban ginshikin sashen Hausa.
Sabo kuma shi ne mai kula da shafin laifin kotu da dan sanda na Leadership Hausa.
Jere ya kuma jajanta wa iyalan mamacin, inda ya bayyana alhininsa game da rasuwar ma’aikacin da suka yi aiki tukuru, cikin aminci.
Ya ce rasuwarsa babban rashi ne ga daukacin sashen na Hausa da kuma kamfanin jaridar Leadership baki daya.
Ya roki Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta masa kurakuransa, Ya kuma sada shi da Aljanatul Firdausi.
“Allah ya bai wa iyalansa juriyar wannan rashi da suka yi.”
A wani labarin na daban uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta ce za a tuna da mijinta, shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa wanda ya bai wa matasa fifiko.
Da ta ke jawabi a Abuja ranar Talata lokacin da ta kaddamar da shirin Health Initiative for Rural Dwellers (HIRD), ta ce shugaban ya fi sha’awar goyon bayan ga shirin gina matasa.
“Za a tuna da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wacce ke ba da fifiko ga ci gaban matasa.
“Shugaban kasa yana da kishin NYSC. Goyon bayansa ga wannan tsari ya dogara ne a kan imaninsa ga Nijeriya raya, da kuma godiya ga gudummawar wadannan matasa maza da mata. Don haka, iyalina a kodayaushe suna yi wa ’yan uwa masu hidimar kasa da ke aiki a Daura, Jihar Katsina, zuwa liyafar shugaban kasa a lokacin bukukuwan Sallah,” in ji shi.
Ta kuma yi kira ga masu gudanar da wannan tsari na NYSC da kuma ’yan kungiyar da kada su yi kasa a gwiwa wajen inganta hadin kan kasa ta hanyar samar da ingantacciyar hidima ga al’umma ba tare da la’akari da jiha ko wurin aiki ba.
Buhari ta bayyana cewa an samu nasarar bullo da shirin (HIRD), don haka ofishinta ya yaba da aikin ta hanyar bayar da gudummawar “kayan aikin asibitin tafi da gidanka ga shirin domin bunkasa nasarar kungiyar likitoci.”
Ta ce shirin ya yi tasiri matuka musamman a tsakanin mazauna karkara, wanda ke ci gaba da samun yabo daga ciki da wajen kasar nan.
A nasa bangaren, Darakta Janar na masu yi wa kasa hidima (NYSC) Birgediya Janar Yushau Dogara Ahmed ya ce shirin na HIRD ya samo asali ne daga bukatar magance matsalolin kiwon lafiya da ke addabar talakawa a yankunan karkara a fadin kasar nan.
Ya ce shirin wanda aka fara shi a shekarar 2014, wani dandali ne da jami’an kiwon lafiya da suka hada da likitoci, masu hada magunguna, ma’aikatan jinya, da likitocin hakori, da dai sauransu, suke ba da kiwon lafiya kyauta ga jama’a, musamman talakawan karkara.
Ahmed ya ruwaito cewa kawo yanzu sama da ‘yan Nijeriya miliyan uku ne suka ci gajiyar shirin.