Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce sabbin rajistar masu kada kuri’a da ake ci gaba da yi a fadin Nijeriya ta Kai Miliyan 10,487,972 a dai-dai karfe 7:00 na safiyar ranar Litinin, 27 ga watan Yuni.
Hukumar a cikin rahotonta na mako-mako akan cigaban Sabuwar Rajistar zabe wanda aka fitar a ranar Litinin a Abuja, ta bayyana cewa masu kada Kuri’a Miliyan 8,631,696 ne suka kammala rajista
Ta bayyana cewa masu kada Kuri’ar, Mutum Miliyan 3,250,449 sun kammala rajistar ne ta hanyar yanar gizo, yayin da 5,381,247 suka je rumfuna Daban-daban don yin rajistar.
Daga cikin wadanda suka kammala rajistar, akwai Maza Miliyan 4,292,690 sai Mata Miliyan 4,339,006. Daga cikin wadannan adadi, 6,081,456 matasa ne, yayin da 67,171 nakasassu ne.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa INEC ta samu jimillar mutane Miliyan 23,560,043 da suka hada da masu neman sauya sabbin akwatunan zabe da wadanda suke neman sauyin katin nasu Katin da masu neman gyaran bayanan su a katin zaben.
A wani labarin na daban kuma an bukaci a gaggauta tsayar dav takarar tinubu.
Frank a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Lahadi, ya kuma yi kira ga jam’iyyar APC da ta maye gurbin Tinubu a matsayin dan takararta na shugaban kasa idan har tana fatan kasancewa a zaben shugaban kasa a 2023.
Dan gwagwarmayar siyasar, haifaffen Bayelsa ne ya ce hakan ya zama dole biyo bayan zargin rashin kaddamar da takardun makarantar dan takarar APC kamar yadda yake kunshe a kundin INEC wanda ta buga kwanan nan.
Frank, wanda shi ne jakadan kungiyar United Liberation Movement for West Papua (ULMWP) a Gabashin Afirka da Gabas ta Tsakiya, ya ce batun takardar shedar Karatu ta Tinubu ko rashinta, Wannan wani gwaji ne na Tabbatar da cewa Hukumar Zabe ta kasa mai zaman kanta INEC za ta sauke alhakin dake kanta na tabbatar da tantance dan takara ko za tayi bangaranci a babban zaben shekarar 2023 dake gabatowa?
Ya kara da cewa kin gabatar da takardun shaidarsa na karatu kamar yadda doka ta tanada ga wadanda ke neman mukaman siyasa a kasar nan, Tinubu kai tsaye, bai dace ya shiga takarar shugaban kasa ba.