Sabani tsakanin Hukumar leken asiri ta sojin Isra’ila
Tashar talabijin ta 14 ta Isra’ila ta sanar da cewa: dimbin hafsoshi da manyan jami’ai na hukumar leken asiri ta sojin gwamnatin kasar ne sukayi murabus cikinsu harda Daniel Hagari kakakin rundunar sojin kasar.
Tashar talabijin ta Channel 14 ta Isra’ila ta sanar da murabus din manyan jami’an sashen leken asiri na sojojin gwamnatin kasar ciki har da Daniel Hagari kakakin rundunar sojin kasar.
Har yanzu dai ba a bayyana dalilin yin murabus din da kuma sauye-sauyen na kwatsam din ba, sai dai a ‘yan makonnin nan an sami rashin jituwa sosai a majalisar ministocin birnin Tel Aviv, musamman tsakanin Firaminista Benyamin Netanyahu da ministan yakin Isra’ila Yoav Galant.
Tashar talabijin ta 14 ta gwamnatin Sahayoniya ta bayyana cewa, dimbin jami’an sashen leken asiri na sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi murabus alokaci daya.
Rahoton yana nuni da cewa dalilin murabus din ze iya zama rashin amincewar jami’an kan siyasar natanyahu dayake yi dan kare kansa.
Tashar talabijin din ta kara da cewa, wannan murabus din na nuni da cewa akwai sabani a ma’aikatar leken asiri ta rundunar sojin da ke karkashin kulawar kakakin rundunar, Daniel Hagari.
kafofin yada labaran Isra’ila sun bayyana a jiya cewa Benny Gantz ya je birnin Washington a wani mataki na ba zato ba tsammani ya kuma yi watsi da ka’idojin da majalisar ministocin hadin gwiwa ta amince da shi ba tare da hada kai da Netanyahu ba, kuma yaje dan ganawa da jami’an fadar White House ba tare da izini ba game da shawarwarin kan yakin Gaza. Daga nan kuma ya tafi Landan.
Buba nan👇👇