Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga tsakanin gwamnatin kano da ‘yan kasuwa a jihar kan rusau da gwamnati ke yi bayan ganawarsa da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.
Idan dai za a iya tunawa, Gwamna Abba Kabir Yusuf a cikin daren ranar Asabar ya rusa wasu gine-gine a Otal din Daula da kuma sansanin Hajji da ke cikin birnin Kano.
An rusa gine-gine na miliyoyin nairori kamar dai yadda aka rusa wani ginin kasuwa mai hawa uku da ke da shaguna 90 a kan titin Race Course, a unguwar GRA ta Nasarawa. Gwamnatin ta bayyana gine-ginen ne a matsayin haramtattu.
A ranar Asabar, Gwamna Yusuf ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da rusa gine-ginen da gwamnatin ta yi imanin cewa haramtattu ne a jihar.
Wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnatin jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ta ce za a ci gaba da aikin rusau.
Bayan faruwar wannan lamarin, Gwamna Ganduje ya garzaya don ganawa da shugaban kasa a ranar Litinin a fadar shugaban kasa domin yi masa bayani kan irin abubuwan da ke faruwa a jihar ta Kano.
“Tinubu ya ba da umarnin a dakatar da rusau, hakan bai dace ba, yana haifar da asara ga ‘yan Nijeriya,” in ji wata majiyar da ta so a sakaya sunanta kuma tace Tinubu ne ya bayyana hakan.
Shugaba Tinubu, Ya kuma bukaci jami’an tsaro da su dakile duk wani yunkuri na cigaba da rusau din a Jihar.
Da aka tuntubi gaskiyar wannan batu da aka ce ya fito daga fadar shugaban kasa, Tofa ya shaida wa jaridar Politicsdigest cewa: “har yanzu ana ci gaba da rusau, gwamnati ta kuduri aniyar kwato kadarorin jama’a da aka sayar ko aka wawure.”