Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kori jami’anta bakwai a jihar Imo
Rundunar ‘yan sandan jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya ta kori jami’anta bakwai waɗanda aka samu da laifukan da suka ƙunshi cutar da al’umma da razanarwa da yi wa jama’a ƙwacen kuɗi, da bincikar wayoyin jama’a ba bisa ƙa’ida ba, tare kuma da saɓa wa umarnin babban Sifeton ‘yan sanda na ƙasar kan kyakkyawar mu’amala da sauran al’umma.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Mike Abattam ya fitar, ya ce an kama jami’an ne ranar 8 ga watan Nuwamban 2022 a harabar wani banki da ke birnin Umuahia na jihar Abia, a lokacin da suke tsaka da aikata munanan laifukan karɓar kuɗi a wajen mutanen da ba su aikata wani laifi ba.
Ya ƙara da cewa an gurfanar da su a gaban kotun Majistare da ke birnin Owerri, inda aka same su da laifi, inda kuma nan take rundunar da kore su daga bakin aiki.
Mista Abattam ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarni ga duka shugabannin ofisoshin ‘yan sanda da ke faɗin jihar da su tabbatar da cewa sun gargaɗi jami’an da ke aiki a ƙarƙashinsu kan aikata makamancin wannan laifi,.
Yana mai cewa duk jami’in ɗan sandan da aka samu da hannu a irin wannan laifi to zai fuskanci matakin ladabtarwa.