Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta fitar da sanarwar tsaurara matakan tsaro a makarantu da asibitoci a daukacin kasar.
Sanarwar na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun karuwar ayyukan ta’addanci.
Sanarwar da rundunar ta fitar a yau Lahadi, ta umarci dawo da shingen bincike da zai bayar da damar duba ababen hawa a lokacin da za su shiga gine-ginen gwamnati.
Sai dai shugaban ‘yan sandan ya umarce su da yi aikin cikin kwarewa ba tare da cin zarafin ‘yan kasa ba.
Wannan sabon matakin na rundunar’yan sanda zuwa ne a daidai lokacin da kasar ci gaba sa tunkarar babban zaben 2023.
Al’umma a Nijeriya da ma masu rajin kare su na martani a game da wannan mataki na dawo da shingen bincike, wanda suka ce duk da alkawarin da mahukuntan kasar suka yi na dawo da da’a a tsakanin jami’an ‘yan sanda har yanzu suna ci gaba da tsohuwar dabi’arsu wacce a shekarar 2020 ta jefa kasar cikin hargitsi har ta kai ga zanga-zangar ENDSars.
A baya-bayan matsalar tsaro na ci gaba da babbar barazana a Nijeriya, inda ‘yan ta’adda suka lashi takobin sace shugaban kasar, Muhammadu Buhari dungurugum.
Ko a satin daya wuce an kai hare hare a kauyukan katsina mahaifar shugaban Kasa Buhari, bayan hare haren da aka dingi kaiwa babban birnin tarayyar Abuja inda Shugaban kasan ke kwana.
Masana tsaro nakallon lamarin babban duk da da alamun gwamnati na yima lamarin kallon ko in kula.
Ko harin da aka kai kurkukun kuje dake Abuja ya Isa gwamnati ta shiga taitayin ta Inji wani mai sharhin lamurran yau da kullum.
Source: Leadership