Rundunar yan sanda a jihar Sokoto ta yi jan hankali ga jam’iyyun siyasa da masu neman takara gabannin babban zaben 2023.
An bukaci jam’iyyun siyasa da ‘ya’yansu su guji aikata laifukan zabe ko kuma su fuskanci hukunci daidai da tanadin dokar zabe.
Kwamishinan yan sandan jihar Sokoto, Muhammed Usaini Gumel, ya ce idanunsu na kan duk wani motsi na yan siyasa a wannan lokaci na yakin neman zabe.
Gabannin babban zaben 2023, kwamishinan yan sandan jihar Sokoto, Muhammed Usaini Gumel, ya ja hankalin jama’a da su taimaka wajen tabbatar da daidaito a tsakanin masu zabe, daukacin masu neman takara, jami’an gwamnati da na tsaro.
Kwamishinan a wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, Sanusi Abubakar, ya gargadi yan siyasa kan aikata laifukan zabe da aka lissafa a dokar zabe, jaridar Punch ta rahoto.
Wasu daga cikin laifukan zabe Wasu daga cikin laifukan zaben kamar yadda Gumel ya bayyana sun hada da kada kuri’u daga bangaren mutanen da basu da rijista da yin zabe a sirrince.
Sauran sun hada da siya da siyar da kuri’u, rashin bin tsari a rumfunan zabe, zabe ba daidai ba da kuma yin jawabin karya, lalata kayan zabe da yiwa jami’an zabe sojan gona, rahoton PR Nigeria.
Dangane da haka, rundunar ta jaddada jajircewarta na yin maganin wadanda suka saba kamar yadda dokar zabe da kundin tsarin mulkin Najeriya suka tanadar.
Jawabin na cewa: “Rundunar na amfani da wannan damar don sanar da yan kasa masu bin doka a jihar musamman jam’iyyun siyasa da yan takara da su ja hankalin mambobi da mabiyansu a kan su dunga lura da nusar da su game da aifukan zabe da aka ambata.
“A karshe, rundunar na son nuna godiyarta kan hadin kai da take ci gaba da samu daga dukkanin masu ruwa da tsaki musamman wadanda suka halarci taron masu ruwa da tsaki da gudunmawa da fahimtar junan da rundunar ke samu a yayin yakin neman zaben jam’iyyun siyasa. “
Musamman, rundunar na farin ciki da gudunmawar da take samu daga kungiyar NBA, bangaren shari’a, kafofin watsa labarai, NUJ, Hukumar NBC na yanki da kuma hukumar INEC kan abubuwan da suke yi wajen wayar da kan jama’a da kuma karfafa masu gwiwa kan ci gaba da yada taken rundunar yan sandar.”
Tinubu ya sha alwashin kawo karshen ta’addanci a arewa idan ya lashe zaben 2023.
A wani labari na daban, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya dauki alkawarin magance matsalolin fashi da makami da ta’addanci a yankin arewacin Najeriya idan har ya yi nasara a zabe mai zuwa.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 12 ga watan Disamba yayin da ya kai ziyarar jaje ga al’ummar yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.