Rundunar sojan ruwan Najeriya ta ce ta kama ɗanyen mai da dama na sata.
Rundunar Sojin ruwan Najeriya ta ce rundunarta mai yaƙi satar ɗanyen mai ta yi nasarar kamawa da ƙwace jiragen ruwa na kwale-kwale da ke ɗauke da ɗanyen man Najeriya da aka sace.
Rundunar sojin ruwan ta ce rundunar Dakatar da Ɓarawo mai farautar ɓarayin wadda aka ƙaddamar a farkon Afrilu ta samu nasarori da dama na kama ɓarayin mai a yankin kudu maso kudancin Najeriya mai arzikin fetir.
Sanarwar da rundunar ta fitar ranar Lahadi ta bayyana nasarorin da rundunar ta samu.
Rundunar ta ce jirgin ruwanta na Pathfinder ya kama wasu jiragen ruwa guda tara na Cotonou da ke ɗauke da man dizel a yankin Andoki da Bille a ranar 5 ga Afrilu. Rundunar ta kuma kama man tataccen mai wanda adadinsa ba a tantance ba a yankin Bonny.
An kuma gano wata rijiyar mai da cibiyar da ake tace man girki a Ketoru.Rundunar ta kuma kama wani jirgi ɗauke da ɗanyen mai lita 520,000 da ake zargin sato shi aka yi a yankin Warri.
Rundunar ta ce ta kama tataccen mai na dizel lita 6,000 a yankin Yanagoa na jihar Bayelsa da kuma wasu motocin dakon ko wacce ɗauke da lita 35,000. Ta kuma kama ɗanyen mai lita 50,000 da lita 150,000 da lita 30,000 da ake zargin na sata ne a yankin Warri a ranar 15 ga watan Afrilu.