Akalla gwamnoni hudu ne suka rufe kasuwanni a jihohin su a kokarinsu na dakile aikin ta’addan cin.
Kwanaki kadan bayan rufe kasuwanni a wasu yankunan karkara a Sakkwato, ‘yan bindigan sun nemi abasu abinci don sakin wadanda suka yi garkuwa da su.
Wani mazaunin Sabo Birni, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu yadda yaron wani makwabcinsa aka sako shi bayan sun bada kayan abinci.
“Sun sace ‘yar wani mutum a kauyen mu, bayan ya gaza biyan kudin fansarta sai suka nemi ya kawo shinkafa mudu 10 a matsayin fansarta, kuma sun cika alkawarin da suka dauka.
Wani mazaunin Sakkwato ya shaida wa wakilinmu yadda ’yan bindigan suka nemi kayan abinci da abin sha don sakin wani direba da suka sace.
“Da farko sun nemi Naira miliyan 15 kafin daga baya su amince su karbi N600,000.
“ Sun nema a siyan musu buhunan shinkafa, abin sha (Fearless), katan spaghetti, sigari sannan akai musu sauran canjin.
Har yanzu ana kokarin tara kudin, ”inji shi.
A wani labarin na daban yau ne ake cika shekaru 20 da abkuwar mummunan harin ta’addanci na 9.11 a kasar Amurka. Bayan abkuwar lamarin a shekarar 2001, kasar Amurka ta fara kai hari kasar Afghanistan, bisa fakewa da yakar ta’addanci.
Sai dai zuwa yanzu bayan da kasar Amurka ta kashe dala fiye da triliyan 2, da asarar rayukan sojojin kasar fiye da 2000, ta fahimci cewa, ba za ta iya ci gaba da yakin ba.
Don haka ta janye sojojinta daga Afghanistan, inda suka haddasa wani yanayi mai matukar muni ta fuskar jin kai: Inda ta lalata kasar, tare da halaka ‘yan Afghanistan fiye da dubu dari daya