Biyo bayan rufe jami’ar jihar Kaduna da gwamnatin jihar tayi bisa abin da ta kira rashin bin doka da oda da yunkurin haifar da rashin zaman lafiya daga bangaren daliban wanda hakan ya sanya dalibai guda dubu goma sha biyar (17,000) zaman giden iyayensu dole.
Gwamnatin jihar tace babu ranar bude jami’ar har sai lokacin da mahukunta jami’ar suka sanar da komai ya kankama.
A kwanan baya ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da karin kudin makarata a jami’ar dama sauran manyan makarantun jihar baki daya.
A zantawar da wakilinmu yayi da kwamishinan ilimi na jihar Kaduna ta wayar tarho Dakta Shehu Mohammed Makarfi, ya bayyana cewa karin kudin wani mataki da gwamnati ta fara dauka na kara inganta harkar ilimi a fadin jihar
A hira da wakilinmu yaui da wani malami a jami’ar ta (KASU) yayi wanda ya bukaci a sakaya sunansa yace jami’ar tana da dalibai dubu goma sha bakwai (17,000) daga cikin su guda goma sha tara (19,000) ‘yan asalin jihar Kaduna ne, wanda kuma mafiya yawa mahaifansu masu karamin karfi ne.
Binciken da Leadership Ayau, tayi ya nuna cewa karin kudin makarantar zai sanya dubban dalibai aje karatusu.
Hasalima, wasun su ba za su samu damar iya kammala karatun ba duba da yadda rayuwarsu take..
Sai dai karin kudin makarantar ya janyo batutuwa da dama, inda jama’a su ke ta korafi tare da kokawar rashin dacewar karin kudin. Jama’a da dama sun nuna rashin dadinsu inda suka bukaci gwamnatin jihar data kara duba lamarin.
Hakazalika, Leadership Ayau, ta gano cewa a sabon karin kudin da gwamnatin tayi dalibin dake karatu a jami’ar jihar Kaduna ( KASU) zai biya kudi naira dubu dari da hamsin (150,000 )maimakon naira dubu ashirin da hudu ( 24,000) da ake biya a baya. Yayin da mai karatun difiloma zai biya dubu saba’in da biyar (75,000,) sai kuma mai karatun matakin babbar difiloma wato HND ya koma naira dubu dari (100,000,) mai matakin NCE shima naira dubu saba’in da biyar (75,000).
A bangare guda kuma kungiyar dalibai ‘yan asalin jihar Kaduna karkashin inuwar kungiyar al’ummar kudancin Kaduna ( SOKAPU) ta bayyana damuwarta dangane da irin rawar da mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ta taka wajen kara kudin makarantar gami da rufe makarantar da gwamnatin tayi inda suka ce tuni suka kawo rakiyarta.
Kungiyar tace kasancewar mataimakiyar gwamnan ta fito daga shiyyarsu amma ta kasa tabuka komai akan lamarin duba da cewa tana daga cikin kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa na lalubo hanyar warware matsalar .
A wata sanarwa da daliban suka rabawa manema labarai mai sanye da sa hannun jami’in hulda da jama’a kungiyar Kwamared ….. sun bukaci daukacin dalibai ‘yan asalin jihar kaduna da suke karatu a manyan makarntu da su shirya fitowa sabuwar zanga-zanga domin nuna rashin amincewa da matakin gwamnati na kara kudin makaranta gami da rufe musu makarantar, wanda hakan a cewarsu zai zamar musu mafita wajen magance matsalar.
Sunce zasu fito babu gudu babu ja da baya zasu rufe hanyoyi koda kuwa gwamnati zata karar da su ne sai sun cimma barunsu na yin allah wadai da gwamnatin.
Kwamared… yace sunsha mamakin irin kalaman da Dakta Hadiza tayi wajen zaman kwamitin inda suka ce tana daga cikin sahhun gaba waje kawo batun karin kudin, a cewarsu, daliban kudancin kaduna sun nisanta kansu da ita a matsayinta na wakiliyarsu a gwamnatin jihar kaduna.
Suma kungiyar malaman jami’ar ta KASU wanda suma suke takun saka da gwamnatin jihar sun tofa albarkacin bakin na nuna rashin jin dadinsu akan matakin gwamnatin na kara kudin makarantar.
A wata sanarwa da shuganan kungiyar Dakta Petre Adamu, ya rabawa manema labarai yace dayawan dalibai za su bar makarantar sakamakon iyayensu ba za su iya biyan kudin makarantar ba.
Akan hakan ,Shugaban, ya ja hankalin gwamnatin jihar Kaduna da ta janye batun karin kudin makarantar, ta kuma gana da masu hannu da shuni kan lamarin, kamar yadda yake a dokar makarantar domin samar da mafita.
Sanarwa tace “Hakkin gwamnati ne samarwa da ‘yan kasa ilimi, ba wai alfarma ba ce yin hakan, kuma yin hakan na kan wuyan gwamnati ne ba iyaye ba, kamar yadda ya ke a tsarin mulkin dokokin kasar nan”
Wakilinmu ya zanta da bangarorin al’ummar jihar, da yawansu su bayyana cewa, a irin wannan lokacin da a ke fama da matalar tsaro, matsalar garkuwa da mutane da aikata laifuka a cikin al’umma, bai kamata gwamnati ta dauki wannan matakin ba wanda zai iya lalata harkokin ci gaban jihar baki daya.