Rudani ya Kunno kai A Jam’iyar APC Bayan Nisanta Kanta Daga Batun Tsige Mai mala Buni.
Jam’iyar APC mai mulki A Najeriya na cikin rudanin bayan da ta nisanta kanta da rahotanni da ake yadawa na sauke gwamnan jihar Yobe mai mala Buni a matsayin shugaban riko na Jam’iyar ta Apc ,
Wasu majiyoyin labaran sun bayyana cewa shugaban Najeriya mohammadu buhari ya goyi bayan sauke shugaban riko din na Jam’iyar APC kafin barin sa Najeriya zuwa birnin London domin duba lafiyarsa, tare da sanar da gwamnan jihar Najer Abubakar Bello a matsayin wanda zai maye gurbinsa.
Tuni dai aka ga jami’an tsaro kewaye da sakatariyar jam’iyar ta kasa dake birnin Abuja a daidai lokacin da ake ci gaba da yada jita-jitar sauke Buni, kuma sun ce an gayyato su ne domin su dawo da doka da oda, kuma sun rufe babbar hanyar dake isa zuwa ga Hedkwatar ta APC.