Rivers – Bayan kwashe kwanaki 62 a garkame, Babbar Kotun jihar Ribas karkashin jagorancin Mai Shari’a Chinwendu Nworgu ta amince da buƙatar ba da Belin ɗan majalisar wakilan tarayya, Honorabul Farah Dagogo.
Ledership ta ruwaito cewa Dagogo,wanda ya nemi takarar gwamna a jam’iyyar Peoples Democratic Party wato PDP, na fuskantar shari’a ne kan zargin aikata babban laifi.
Ɗan majalisar ya shiga hannun hukumomi ne a ranar 22 ga watan Afrilu, 2022 a wurin taron tantance yan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP wanda ya gudana a Patakwal.
An kama shi ne ƙasa da awanni huɗu bayan gwamna Nyesom Ezenwo Wike na jihar Rivers, ya ayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin ɗakko hayar yan daba da ake zargin ƴan asiri ne su tarwatsa taron tantancewa.
A wani labarin an daban kuma mahukunta a Amurka sun sanar da gano gawarwakin ‘yan ci-rani 46 a wata babbar motar daukar kaya da ga alama direbanta ya gudu ya bari a San Antonio da ke tsakiyar jihar Texas kusa da iyaka da Mexico.
Wannan dai na jerin mafi munin tashin hankali da jihar ta Texas ta gani a baya-bayan nan kan abin da ya shafi ‘yan ci-rani, shekaru 5 bayan fuskantar makamancinsa inda aka tsinci gawar gomman bakin haure cikin shekarar 2017.
Shugaban ‘yan kwana-kwana a yankin da abin ya faru Charles Hood, ya ce an tarar da wasu mutane 16 da rayukansu a motar, ciki har da kananan yara 12 kuma yanzu haka suna samun kulawa a asibiti.
Mahukuntan jihar dai basu bayar da cikakken bayani kan kasashen da ‘yan ci-rani suka fito ba haka zalika babu bayanai kan shekarunsu ko kuma jinsin su.