Gwamnan Jihar Rivers da ke Najeriya, Nyesom Wike ya musanta sahihancin bayanan da ke cewa, gwamnatin Jihar ta rusa Masallaci a birnin Fatakwal, yana mai cewa, wasu bata-gari ne suka kirkiri rahotannin domin haifar da kiyayya.
A lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a wurin da aka ce an rusa Masallacin na Trans Amadi, Gwamnan ya ce, babu wani Masallaci a wurin, a don haka babu wani gini da aka rusa.
Gwamnan ya ce, ya samu kira ta wayar tarho daga dimbin fitattun mutane a Najeriya game da labarin da ya ce, na kanzon kurege ne wanda kuma aka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta.
Gwamnan ya yi karin bayani, inda yake cewa, wasu mutane sun fara aza tubulin haramtaccen gini a wurin duk da cewa, ba su samu izinin gudanar da aikin ginin ba a hukumance.
Maginan sun maka gwamnatin jihar a kotu amma ba su yi nasara ba kamar yadda Wike ya shaida wa manema labarai.
Gwamnan ya kalubalanci al’ummar Musulmin jihar Rivers da ta nuna masa wurin da aka rusa Masallaci a fadin jihar.
Sai dai a zantawarsa da Sashen Hausa na RFI Alhaji Yakubu Aliyu, ya bayyana cewa, gwamnatin ta rusa musu Masallacin Juma’ar wanda suka sayi filinsa akan Naira miliyan 10 da dubu 800 shekaru 10 da suka wuce.
Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken bayanin Alhaji Yakubu Aliyu, daya daga cikin masu kula da Masallacin.