Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wasu mutane uku da ake zargi da yunkurin tayar da rikici yayin da masu sayar da magunguna suka fara kwashe kayansu zuwa sabuwar kasuwa da ke Dangauro a jihar Kano.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Hussaini Gumel, ya shaidawa manema a Kano ranar Lahadi cewa an kama wadanda ake zargin ne sakamakon rufe bakin filazar Mai-Karami da ke kasuwar a Kano.
Gumel ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da wasu ‘yan kasuwar ke kwashe kayayyakinsu zuwa sabuwar kasuwarsu da ke birnin Kano Economic City, dangwauro, a wajen birnin na Kano.
Ya bayyana cewa wasu ‘yan bata-gari sun yi yunkurin haifar da rikici a wurin, amma ba tare da bata lokaci ba ‘yan sanda suka tarwatsa su.
Duba Nan: An Tabbatar Da Matsayar Dan Takarar Shugaban Kasa Obi
Ya ce, manufar wadanda ake zargin shi ne su yi awon gaba da kaya tare da kutsawa cikin wasu shaguna da ke Plaza.
Kwamishinan ya ce wadanda ake zargin yanzu haka suna hannun ‘yan sanda, ya kara da cewa ya bayar da umarnin bayar da “ tsaro a filin Filazar”.
Ya ce an tura karin jami’an ‘yan sanda domin samar da tsaron da ake bukata a yayin da ake ci gaba da jigilar kayayyaki zuwa sabuwar kasuwa.
Source: LEADERSHIPHAUSA