Rikici kan shugabanci a Masallacin Darul Hadith da ke Tudun Yola a Kano ya kawo cikas yayin Sallar Jumu’a ranar 6 ga watan Janairu.
Sahihan bayanan da muka samu sun nuna cewa bayan wannan matsalar rikici da aka samu, jami’an yan sanda sun ba da tsaro har aka gama Sallah.
Kakakin yan sanda, Abdullahi Kiyawa, yace tuni aka gayyaci bangarorin biyu domin lalubo bakin zaren.
Rikici kan shugabanci a Masallacin Darul Hadith na marigayi Sheikh Dakta Ahmad Ibrahim BUK dake Tudun Yola a Kano, ta kawo tsaiko yayin gudanar da Sallar Jumu’a ranar 6 ga watan Janairu, 2023.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa rigimar ta ɓarke ne lokacin da wasu daga cikin manyan Masallacin suka hana sabon Limami wucewa, yayin da zai shiga ya hau Mimbari don jagorantar Sallar Jumu’a.
Wasu bayanai da ake yaɗa wa sun nuna cewa fusatattun mutanen sun hana Limamin hawa Mimbari ya yi huduba, lamarin da ya kawo tsaiko yayin Sallar mai dumbin falala.
Limamin, wanda aka tsara zai jagoranci Sallar a jiya, ya kama hanyar shiga wajen da aka ware wa Liman a Masallacin, ba zato mutanen suka tare shi, an ce har rigarsa suka rike.
Sakamakon wannan takaddama da aka samu, nan take jami’an tsaro suka shiga tsakani, suka kewaye Masallacin don tabbatar da doka da oda, hakan ya sa wasu Masallatan suka kama gabansu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, yace ba tare da bata lokaci dakarun ‘yan sanda suka kai ɗauki bayan samun kishin-kishin din abinda ke faruwa.
“Nan take Kwamishinan yan sanda ya umarci a tura karin jami’ai Masallacin domin tabbatar da bin doka da oda.”
“Jami’an sun dawo da komai kan hanya kuma an gudanar da Sallah ba tare da wata matsala ba.
A halin yanzun hukumar ‘yan sanda ta gayyace bangarorin biyu domin gano bakin zaren.” – Abdullahi Kiyawa.
Tuni dai mazauna yankin Amguwar Tudun Yola suka ci gaba da harkokin gabansu bayan abinda ya faru a Masallacin.
Dalibai mata a BUK sun sake shiga tasku
A wani labarin kuma Barayi Sun Shiga Dakin Kwannan Dalibai Mata A Jami’ar Bayero Da Ke Kano
Jami’ar dai ta dawo daga hutun kirsimeti da sabuwar shekara a farkon satin nan da muke ciki wanda hakan yasa akwai karancin dalibai a dukunan kwanan.
An ce barayin sun shiga Hostel din Nana Hall, suka yi barna mai tarin yawa da ta hada da sace wayoyi da wasu kayan amfanin dalibai.
Source:LegitHausa