Rikici a jam’iyyar APC na neman taɓa shirin Kamfe a wasu jihohi, jihar Enugu ta nemi kada a tura mata kudin Kamfen na Tinubu.
Ɗan takarar gwamna a jihar Enugu karkashin APC yace ana tsammanin kuɗin ka iya wargaza jam’iyyar idan aka zo batun raba su.
Mista Nnaji zai gana da shugagan APC na ƙasa yau Litinin, washe gari kuma zai gana da Tinubu kan lamarin.
Ɗan takatar gwamnan jihar Enugu a inuwar jam’iyyar APC, Uchenna Nnaji, ranar Lahadi yace suna hasashen rikicin da ya addabi jam’iyya na da alaƙa da kwaɗayin kuɗin Kamfe da za’a turo wa jihar.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Nnaji ya yi wannan jawabi ne a wurin wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a Ofishin jam’iyya na shiyyar kudu maso gabas.
Ɗan takarar ya ce matukar kuɗin kamfe daga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, mai neman kujerar shugaban kasa zasu wargaza APC-Enugu, to maimakon haka ya kamata a rike kuɗin har sai bayan zaɓe.
A ruwayar Vanguard, Mista Nnaji yace: “Rikici da ya addabi APC a Enugu duk a kan kuɗin Kamfen ɗin Tinubu ne, waɗan da ake kira masu ruwa da tsaki na faɗi tashin babbake kaomai game da rabon kuɗin.”
“Bamu bukatar kuɗin Kamfe na ɗan takarar shugaban ƙasa, Bola Tinubu, domin tunkarar babban zaɓen 2023, da taimakon Allah zamu yi amfani da kuɗin mu na Enugu wajen shirya wa zaɓen, bayan zaɓe, jam’iyya zata dawo mana da kuɗin.”
“Bayan wannan taron na gaggawa, zan tafi Abuja gobe (Litinin) domin na faɗa wa shugaban APC na ƙasa bamu bukatar kuɗin kamfe. Washe gari zan gana da Tinubu kuma zan maimata masa haka.”
Bugu da ƙari, ɗan takarar gwamnan Enugu a APC ya yi kira ga ‘Masu ruwa da tsakin Abuja’ su bar rikici su dawo gida domin haɗa karfi da karfe wajen haɗa wa jam’iyya magoya baya gabanin zaɓe.
A cewarsa, tare da shugaban jam’iyya a Enugu, Agballah da ‘yan tawagarsa sun karaɗe baki ɗaya gundumomi 184 da yankuna 204 dake sassan ƙananan hukumomi 13 na jihar duk a shirin tunkarar 2023.
Ya kuma koka kan yadda aka canza wa jam’iyyar akala daga kokarin lashe zaɓe, wasu marasa kishi na kokarin tsige shugabanni watanni shida kacal kafin babban zaɓe.
A wani labarin kuma Gwamnan APC Ya Fallasa Wanda Wike da Wasu Gwamnoni Suka Amince Ya Gaji Buhari a 2023.
Gwamnan Ebonyi yace baki ɗaya takwarorinsa na yankin kudancin Najeriya bakinsu ɗaya kan wanda zai gaji Buhari a 2023.
Gwamnan ya bayyana cewa Wike da sauransu sun zauna tun a baya sun cimma matsaya kan tsarin karɓa-karba.
Source: LEGITHAUSA