Gwamnatin Jihar Ribas karkashin jagorancin Gwamna Siminalayi Fubara tare da hadin guiwar Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) sun karbi bakuncin manyan ‘yan kasuwa a kokarin gwamnatin na habbaka tattalin arziki ta bangaren saka hannun jari a bangaren alfanun albarkatun cikin ruwa.
Taron bitar na kwana daya wanda hukumar NIS da gwamnatin jihar Ribas suka shirya, ana sa ran zai samar da wata dama da za ta taimaka wa jihar Ribas da gwamnatin tarayya wajen binciko tarun albarkatun arziki da ke cikin teku.
Mukaddashiyar Kwanturola Janar ta Hukumar NIS, Caroline Wuraola Adepoju, wadda ta halarci taron bitar da aka yi a Kamfanin Gwamnan Jihar, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Dakta Tammy Danagogo ya wakilta, ta yaba wa tsare-tsaren Gwamnatin tarayya na sake habbaka tattalin arziki wanda ya kai ga amincewa da kafa ma’aikatar tattalin arziki ta ruwa ta tarayya don fadadawa da kuma karkata tattalin arzikin Nijeriya daga man fetur da iskar gas zuwa albarkatun ruwa da tekun da ke kewayen Nijeriya.
Jihohin da ke zagaye da ruwa da ‘yan gabar teku sun hada da: Rivers, Bayelsa, Delta, Edo, Ondo, Lagos, Anambra, Cross Ribas, Akwa Ibom, Kebbi da Neja.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai tsohon Kwanturola Janar na Hukumar NIS, Dakta David Shikfu Paraddang; Shugaban Elshcon Group, Dakta Emi Membere – Otaji; Mataimakin Shugaban Kungiyoyin Kasuwanci, Masana’antu, Ma’adinai da Aikin Noma, Majalisar Dillalan Jiragen Ruwa wanda Mista Glory Onojedo ya wakilta; Shugaban hukumar kula da tashar jiragen ruwa ta Nijeriya (NPA), Mista Michael Adamu; Kodinetan shiyyar NIMASA ta Kudu-maso-Kudu, Mista Yusuf Barde; Shugaban kamfanin Sigma Nigeria Limited, Dakta Soky Amachree da shugabannin masana’antu masu zaman kansu.
Mahalarta taron sun yabawa Kwanturolan hukumar NIS mai kula da reshen Jihar Ribas da tawagarsa bisa shirya wannan taron karawa juna sani a lokacin da ake bukatar taron domin samun kyakkyawar fahimta akan sabuwar ma’aikatar ta yadda masu zuba jari za su nutsu da ma’aikatar da kuma tsare-tsarenta.
Source LEADERSHIPHAUSA