Gwamnatin jihar Ribas ta aikawa Lee Maeba takarda cewa an karbe wani fulotinsa a Fatakwal.
Sanata Lee Maeba ya rasa filin da ke unguwar GRA ne watanni shida bayan Gwamna ya mallaka masa.
Tsohon Sanatan shi ne Shugaban kwamitin da ke yakin neman zaben Atiku Abubakar a jihar Ribas.
Gwamnatin jihar Ribas ta karbe takardar fili watau CoC da aka ba tsohon ‘dan majalisar dattawa, Sanata Lee Maeba a unguwar GRA a Fatawakal.
Punch a rahoton da ta fitar dazu, ta bayyana cewa Sanata Lee Maeba jigo a PDP, shi ne shugaban kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar a jihar Ribas.
A wata takarda da ma’aikatar filaye da safayo ta aikawa Maeba a ranar Laraba, 2 ga watan Nuwamba, an sanar da shi an karbe filin da aka taba ba shi.
Darektar rikon kwarya ta sashen mallakar filaye ta ma’aikatar filaye da safayo, Ochiagha Onyebuchi ta rubuta takardar a madadin babbar sakatare.
“An umarce ni in sanar da kai cewa an karbe filinka da ke kan Plot 20A, Golf Course Layout, tsohuwar GRA, Fatawal kamar yadda wallafar da gwamnatin jihar Ribas mai lamba No. 22 Vol. 58 na 20 ga watan Satumba 2022 ta nuna. Sakataren din-din-din ya na mai aiko da gaisuwarsa.”
Wata 6 da suka wuce aka ba ni filin Da aka yi magana da tsohon Sanatan na Kudu maso gabashin Ribas, a fusace ya tabbatar da cewa gwamna ne ya ba shi filin watanni shida da suka wuce.
Tun da aka gudanar da zaben fitar da gwani na ‘dan takarar shugaban kasa, aka samu sabani tsakanin Atiku Abubakar da ya yi nasara da Nyesom Wike.
Ana zargin gwamna Wike yana neman ganin bayan ‘yan PDP da ke tare da Atiku a Ribas.
Bayan Celestine Omehia ya ziyarci ‘dan takaran shugaban kasa a PDP, sai aka ji cewa majalisar dokokin Ribas ta cire masa matsayin tsohon Gwamnan jihar.
Gwamnati ta bada umarni an rufe gidan man Hon. Chinyere Igwe, wanda yanzu ‘dan majalisar wakilan tarayya ne wanda yake goyon bayan Atiku Abubakar.
Sauran magoya bayan Atiku sun hada da tsohon mataimakin shugaban majalisa, Rt. Hon Austin Opara da Austin Sekibo da aka ji Gwamnan ya taso a gaba.
Source:legithausang