Wani rahotan da kamfanin dillacin labarai na Reuters ya fitar ya nuna yadda sojojin Nigeria ke tilastawa mata zubar da ciki.
Rahotan Reuters da ta fitar ya ja hankalin duniya inda majalissar Dinkin Duniya ma ta shiga batun.
Hukumar rundunar Sojojin Nigeria ta musamntan zargin wani rahoto da kamfanin dillacin Labarai ya fitar na zargin sojointa da aikata laifin tilastawa mata zub da ciki.
Duk da musantawar da hukumomin tsaron Najeriya suka yi, Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin tarayya da ta binciki rahoton da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar.
Reuters ya rawaito cewa sojojin Nigeria na tilastawa mata masu juna biyu da ake alakantawa da mayakan Boko Haram da zubar da ciki.
Reuters a ranar Laraba, 7 ga watan Disamba, 2022, ya yi zargin cewa sojojin Najeriya na gudanar da wani tsari na tilasatawa mata zubar da ciki a asirce da ba bisa ka’ida ba a yankin arewa maso gabas tun 2013.
Rahoton ya yi zargin cewa akwai ‘yan mata kusan 10,000 wadanda yawancinsu mayakan Islama na boko haram sukai musu fyade, sannan sojojin kuma suka tilasata musu zubar da cikin.
A wani Rahotan jaridar The Punch tace rundunar sojin ta musanta rahoton inda ta ce ba gaskiya bane.
Har ila yau, shugaban rundunar sojan ya yi ikirarin cewa rahoton wani yunkuri ne na yiwa sojoji da kuma kasar zagon kasa.
Yana mai jaddada cewa a ko da yaushe sojoji na kiyaye ka’idojin da’a da ayyukansu.
Majalissar Dinkin Duniya Ta Magantu kan Zargin Sojojin Kasar Da Tilasta Zubar Da Ciki Amma, Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta binciki zargin tilastawa zubar da cikin da sojojin suke yi.
Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ne ya fada hakan a ranar Juma’a yana mai cewa ‘kungiyiyoyi da yawa sun shiga batun lamarin.
Dujarric ya ce: “Ya kamata ace Najeriya ta yi bincike tare da gano musabbabin da ke tattare zargin, in kuma gaskiya ne rahoton, to ya kamata adau mataki akai.
Kakakin ya ce: “Sakatare Janar ya damu kan zarge-zarge na tilasta zubar da ciki da sojojin Najeriya ke yi a kan mata da ‘yan matan da ‘yan Boko Haram suka yi wa fya’de.
“Muna kira ga hukumomin Najeriya da su yi cikakken bincike game da wadannan zarge-zargen kuma su tabbatar da cewa akwai hukunci.”
Source:LegitHausa