Bawko shi ne birni mafi girma na musulmi a yankin arewa maso gabashin Ghana kuma daya daga cikin manyan garuruwan musulmi a Ghana. Al’ummar Shi’a suna da karfi a wannan gari mai makarantun firamare guda uku da masallatai biyu.
Wannan birni yana makwabtaka da kasashen Burkina Faso da Togo, wanda hakan ya sa birnin ya zama daya daga cikin biranen kasar masu bambancin al’adu. An gudanar da wani shiri na rediyo a wannan birni domin isar da sakon hajjin Jagora a fadin kasar Ghana.
Har ila yau, an gudanar da wani shiri a yankin Savanna na Ghana a birnin Bole, gundumar da ke yankin Savanna a arewacin Ghana.
Haka kuma an buga sakon Hajjin Jagoran a birnin Bulgatanga dake tsakiyar yankin arewa maso gabas. Birnin Bulgatanga birni ne mai yawan mabiya addinin kirista, amma duk da haka ya hade tare da mabiya mazhabar Shi’a.
’Yan Shi’a matasa masu karancin shekaru da ke da masallaci da makarantun islamiyya guda biyu don koyar da yara.