A baya-bayan nan Jurgen Klopp na zabar amfani da Joel Matip da Konate don maye gurbin Virgil van Dijk ga tsaron tsakiya maimakon Gomez wanda ko a wasan da Liverpool ta yi canjaras da Tottenham da kwallo 2 da 2 a karshen mako manajan ya yi amfani da Gomez ne mintuna kalilan gabanin karkare wasa.
Bayanai sun ce Real Madrid mai doka La Ligar Spain yanzu haka na kishirwar tsaron tsakiya ne kuma tuni ta fara shirye-shiryen tuntubar dan wasan watakila ta fara Magana da Liverpool a kasuwar musayar ‘yan wasa ta sabuwar shekara.
Sai dai wasu bayanai na daban na nuna cewa abu ne mai wuya Madrid ta iya sayen Gomez a janairu la’akari da yadda za ta makudan kashe kudi wajen dakko Kyllian Mbappe daga PSG ta Faransa.
A wani labarin na daban Gwamnan jihar Kaduna ta Najeriya Nasir El-Rufa’I ya hakikance cewa dole ne a kashe ‘yan bindigar da ke addabar al’umma domin kuwa bai amince da zancen yi musu afuwa ko kuma gyaran halayyarsu ba.
Gwamnan ya bayyana matsayarsa ce a yayin hira da manema labarai a fadar shugaban kasa a jiya Talata jim kadan da kammala ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari.
EL-Rufa’I ya ziyarci shugaban kasar domin yi masa bita kan hare-haren da ‘yan bindiga suka kaddamar kan jama’a a baya-bayan nan a Kaduna, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 40.
Ba a karon farko ba kenan da gwamnan ya sha bayyana cewa, bai dace a yi sulhu da wadannan mutane masu kisan jama’a ba gaira ba dalili ba.