Wata raskwana ‘yar Najeriya ‘yar shekara 13 da haihuwa ta bada mamaki a gasar lissafin yan makaranta ta duniya.
Yarinyar mai suna Nasara James
Dabo ya amsa tambayoyin lissafi guda 34 cikin sakwanni 172 kuma tayi daidai Wannan yarinyar mai baiwa ta lissafi dalibar makarantar Ideal International College ce dake jihar Kaduna.
Wannan raskwana’yar shekara ta ciri tuta a gasar lissafin daliban makaranta ta duniya watau International Mathematical Olympiad.
Nasara James Dabo dalibar makarantar Ideal International College ce dake jihar Kaduna.
A cewar jawabin da shafin Kaduna Affairs na Tuwita ta daura ranar 27 ga Disamba 27, wannan yarinya raskwana ce ta zo na daya kuma ta samu lambar yabo.
Karin Bayani: Yan Ta’adda Masu Yawa Sun Sheka Barzahu Yayin Da Boko Haram Da ISWAP Suka Yi Musayar Wuta Na Awa 14 Nasara James Dabo ta amsa tambayoyi 34 na lissafi cikin dakikai 172.
Ta kayar da sauran masu takara a musabaqar mutum 150. An baiwa Nasara James kyautar lambar yabon zinari bisa wannan gagarumin nasara.
Kalli martanin mutane: Zakariyya Gambo “ALLAH ya karawa YARAN MU basira da hazaka da sani mai anfani a rayuwarsu ya Allah”
James White yace: “Kai yarinyan Nan Allah Kara Mata ilimi da hikima Kuma yasa ta amfani mutane da kasa Baki Daya da ilimin da Allah ya Mata Fatan Alkairi Nasara James Dabo.”
Abdullahi Alhaji Yusuf yace: “Ni ai ko kasheni za ayi sedai akashe dan ban iya mathematics ba Allah yakara basira” Mujaheed Isah
Harun Jogana yace: “Ni fah Ko lokacin da na ke Secondary babu Wadda na tsana kamar Mlmin Maths din mu.
Ai Gaskiya ce Balle na ji yace “X×X²=3.” Fa’eez Aliou Balarabe yace: Inama ace bahausa ce,,,wai su hausawa suna abin gari kuwa
Pwajinti David yace: Allah ya Kara basira. Irin wadannan ne zasu fito da kimar kasar mu ga idon duniya.
Gaskiya muna alfahari da ke sosai
Umar Umar Dogondaji: MashaAllahu irinsu nanan tari tari cikin alummar mu Amma shuwagabbani sun danne su saboda rashi da talauci da suka kakabawa iyayen su.