Darikun addinin Kirista daban-daban na cigaba da gargadin jam’iyyun APC da PDP kada su zabi Musulmi mataimaki, inda suka bayyana zaben musulmin a matsayin rashin tunani.
Darikar Katolika a nata jawabin ta bayyana cewa zaben Musulmi shugaba kuma Musulmi mataimaki rashin tunani ne Yau ko gobe jam’iyyar APC, PDP, LP a NNP zasu sanar da wanda zai yiwa yan takararsu mataimaki.
Hedkwatar Cocin Katolika a Najeriya ta bayyana rashin amincewarta da yunkurin Musulmi da Musulmi suyi shugaban kasa da mataimaki a zaben 2023.
Cocin ta bayyana matsayarta ranar Talata ne a jawabin da Sakatare Janar dinta, Zacharia Nyantiso Samjumi, ya fitar, rahoton TheCable.
Jawabin yace ko lokacin mulkin Soja, da tsarin Musulmi-Kirista akayi amfani.
Yace: “Misali, an yi mulkin Murtala-Obasanjo, Obasanjo-Yar’adua, Babangida-Ebitu Ukiwe, Abacha – Diya.
Hakazalika shugabannin hukumomi daban-daban irinsu Kwastam, Immigration, dss.”
“Lokacin mulkin Sojan Buhari kadai aka samu Musulmi da Musulmi. Hakazalika lokacin zaben Abiola-Kingibe.” Cocin tace asali bai kamata wannan ya zama matsala ba idan kan yan Najeriya a hade yake, amma kan yan Najeriya yanzu ya rabu kashi-kashi.”
“Dubi ga rabuwar kai dake tsakanin yan kasar nan, Tikitin Musulmi-Musulmi ba karamin rashin tunani zai zama ba. ”
“Dubi ga abinda ya faru a Kaduna, da alamun irin wahalan da Kiristocin kudancin Kaduna suka sha zai sake faruwa.”
Cocin ta karkare jawabinta da kira ga jam’iyyun siyasa kada su sake su zabi abokin takara Musulmi.