Ranar Uku Ga Watan Muharram Shekara Ta Bakwai Bayan Hijira, Ranar Da Manzon Allah Sawa Ya Fara Aikawa Sa Wasikun Kiransa Zuwa Ga Kasashen Duniya Domin Kiransu Zuwa Ga Addinin Musulunci
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya habarta cewa, Ranar Uku Ga Watan Muharram Shekara Ta Bakwai Bayan Hijira, Ranar Da Manzon Allah Sawa Ya Fara Aikawa Sa Wasikun Kiransa Zuwa Ga Kasashen Duniya Domin Kiransu Zuwa Ga Addinin Musulunci
بسم الرحمن الرحیم
«وَ ما أَرْسَلْناکَ إِلاّ کَافَّةً لِلنّاسِ بَشِیراً وَ نَذِیراً وَ لکِنَّ أَکْثَرَ النّاسِ لایَعْلَمُونَ»
A irin wannan rana ce uku ga watan Muharram Shekara ta 7 bayan Hijira. Manzon Allah Sawa bayan ya sami sukunin sulhun Hudaibiyya Musulmai sun samu nutsuwa ya yi yunkurin faɗaɗa kiransa domin ya watsu a duniya gaba daya. Inda ya aika da wasiku dadaman gaske zuwa sarakuna da shugabanni al’ummar duniya na wannan lokacin, wanda su wadannan jagororin Al’ummar sun kasu kashi uku ne:
Akwai Sarakunan Kasashe, Shugabannin Addinan Kiristanci Da Yahudawa, da kuma Shugabannin manyan Kabilu da ke kewaye da Yankin Jazirar larabawa Manzon Allah (SAW) ya rubuta wasiku zuwa ga dukkan Jagororin uku.
Manzon Allah ya aika da wasikun da suka kai 26 duk da ba a shekara daya aka aika da wasikun ba amma an fara aika su a wannan ranar ne bisa ga ingantacciyar Riyawa.
Wasu Sunaye Na Jakadun Shugabanni Da Manzon Allah
Sawa Ya Aika Da Su:
Dahiyyah bin Khalifa Kalbi Jakada Ga Ƙaisar, Sarkin Rum.
Abdullahi bin Huzafah Sahmy Jakada Ga Khusrow Parvez, sarkin Iran.
Amr bn Umayyah Dhamri Jakada Ga Najashi, sarkin Habasha.
Hatib bin Abi Baltah Jakad Ga Muƙauƙis sarkin Iskandariya.
Amr bin As Sahmy Jakada Ga Jaifar da Ayaz Azdi: ‘ya’yan Jalandi, Sarkin Oman.
Salit bin Amr Jakada Ga Samamah bin Athal Hanafi
Hauzah bn Ali Hanafi Jakada Ga sarkin Yamamah.
Alaa bin Hazrami Jakada Ga Munzar bin Sawi Abdi, sarkin Bahrain.
Shuja bn Wahhab Asadi Jakada Ga Harith bn Abi Shammar Ghassani, sarkin Takhum a Sham.
Muhajirin Abi Umayyah Makhzoumi Jakada Ga Harith bin Abdul Kalal Hamiri, Sarkin Yaman.
Dukan wadannan Wasiku da aka aika suna dauke da Tambari na Manzon Allah Saw wanda aka Rubuta shi kamar: (الله رسول محمد) kuma ana karanta shi ta kasa ne.
Hakika hasken wahayi ya haskaka ko ina a duniya ta hanyar isar da sakon Annabawa As da Allah Ta’ala ya aiko su zuwa ga halittarsa domin su bayyana masu nauyi da abunda ya doro akansu na hukunce-hukunce Ibada zamantakewa a rayuwarsu ta duniya domin samun rabautarsu duniya da lahira.
Hakan ya sanya Allah Ta’ala ya aiko da Annabawa daya bayan daya wanda na karshensu shi ne Annabi Muhammad Sawa kuma Annabi ya isar da sakon Allah Ta’ala a takaitaccen shekaru 23 na isar da sakonsa wanda kuma ya barwa Al’ummarsa wasu magada nasa wanda Allah Ta’ala ya zaba domin ci gaba da shiriyar da halitta zuwa ga tafarkin Addinin musulunci da shi kadai ne Allah Ta’ala ya aminta da a bauta masa da shi.
Annabi Sawa ya barwa Al’ummarsa Halifofi Imamai da za su gajeshi kuma Imam Husaini As shine na uku a cikin jerinsu wanda muke jajajen kasheshi a goma ga wannan wata ami alfarma da Allah Ta’ala ya hana zubda jini acikinsa amma duk da haka Al’ummar da suke riya cewa su musulmai ne suka aikata hakan ga dan Annabinsu Kuma shugabansu.
Ya zama wajibi ga dukkan Al’umma su tashi tsaye wajen sanin kansu sannan su san me ya hau kansu a wannan takaitacciyar rayuwar domin su samu tsira gobe kiyama.