Ranar rediyo ta duniya Wacce rawa kafar ta taka a rayuwarku ?
Yau ne ake bikin ranar rediyo ta duniya.
Rana ce da hukumar raya al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta kebe musamman don tunawa da tasirin da kafar rediyo ke yi wajen sauya rayuwar jama’a, da kuma irin rawar da take takawa wajen bayar da bayanan abubuwan da ke faruwa a fadin duniya.
A Najeriya da Nijar Kamaru da Chadi, rediyo na ci gaba da jan zarenta, a matsayin kafa mafi yawan mabiya da ta fi bayar da bayanai ga jama’a.
Kwamaret Bishir Dauda, sakataren kungiyar Murar Talaka a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, a yammacin Afirka rediyo ita ce kafa wadda akasarin al’umma ke saurare da samun ilimi da kuma samun nishadi.
Kwamaret din ya ce rediyo na matukar taimakawa kwarai da gaske musamma idan aka yi la’akari da irin shirye-shiryen da ake yi a gidajen rediyon.
Ya ce,”Akwai abubuwa da dama da ni kai na duk da ilimina amma sai a rediyo na kara fahimtarsu, kamar misalin shirye-shiryen da suka jibanci kiwon lafiya ko yanayin zaman takewar al’umma”.
- Wordle: Wasan game din da saurayi ya ƙirƙiro wa budurwarsa don faranta ranta ya samu karɓuwa a duniya
- Wasan kwamfuta na China: Gwamnatin kasar na kokarin hana yara zama kwararrun masu wasan kwamfuta ne?
- TikTok zai dauki mataki a kan bidiyon koyar da cin abinci da basu dace ba
Kwamaret Bishir Dauda, ya ce wani tasirinma na rediyo shi ne kafin ka ga mutum daya yana karanta jarida, sai kaga mutum 100 suna sauraron rediyo saboda saukin ta’ammalin da take da shi.
Ya ce,” Ita fa rediyo baka bukatar komai sai batira wanda idan ka siya ka sa sai suyi maka mako biyu kana jin rediyonka da su, to amma idan mutum talabijin zai kalla ko kuma irin wayoyin salula na zamani zai rinka amfani da su wajen samun labarai to fa su sai da utar lantarki”.
Kwamaret din ya ce, yawanci mutanen karkara da rediyo suka fi samun labarai har ma su san me duniya ke ciki, domin ba kowannesu ne ke da ilimin da zai duba labarai a jarida ko ta wayar salula ba.
Karin bayani
Wasu da BBC ta ji ra’ayinsu a kan irin tasirin da rediyo ke yi a rayuwarsu sun ce ba karamin tasirin ta ke yi ba, saboda ita ce wadda talaka ma zai iya mallaka sannan ba a saka mata wani kudi kamar wayar salula wadda idan kana son ka karanta labari sai ka sayi data.
Masu sauraron rediyon sun ce ko rigar fulani kaje rediyo za ka tarar, kuma tana taimakawa wajen hada kan al’umma sannan ita ba ta karya, ba kamar kafafan sada zumunta ba .