Duk da musantawar hukumar yan sanda da jam’iyyar APC, PDP tace lallai fa an yiwa Buhari rajamu a Kano.
Shugaba Buhari ya tafi jihar Kano kaddamar da katafaren gadar sama da gwamna Abdullahi Ganduje yayi.
PDP ta daura laifin harin da aka kaiwa Buhari kan Tinubu inda tace dama yana son cin mutuncin sa.
Jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta yi Alla-wadai da jifan rajamu da ake zargi an yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar Kano ranar Litinin, 30 ga Junairu, 2023.
Shugaba Buhari ya kai ziyara ta musamman jihar Kano domin kaddamar da wasu manyan ayyuka da gwamnatin jihar ta kammala.
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa wannan duk laifin dan takarar shugaban kasa All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne.
PDP ta ce Tinubu da Ganduje sun shirya cin mutuncin Buhari shi yasa aka yi kokarin hanashi ziyartar Kano tun daga farko.
Kakakin jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, ya bayyana hakan a jawabin kar-ta-kwana da ya fitar da daren Litnin inda yace: “Peoples Democratic Party (PDP) na matukar Alla-wadai da harin da wasu batagari suka kaiwa shugaba Muhammadu Buhari yau a jihar Kano wanda dan takara Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dau nauyi.”
“Jam’iyyarmu ta lura da cewa wannan cikin kaidin da dan takaran APC ke shiryawa don nuna bacin ransa ga shugaban kasa, ya tayar da tarzoma a kasa, ya dakatar da aukuwar zaben 2023, sannan ya mayar da demokradiyarmu koma-baya; bayan lura ba zai iya samun nasara a zaben ba.”
Sai da Ganduje ya shawarci Buhari kada yaje Ologunaba ya kara da cewa sai da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, yayi kokarin hana shugaban Buhari zuwa jihar.
Ya kara da cewa: “Ya kamata a lura cewa dan takaran shugaban kasa na APC ya dade yana fito-na-fito da shugaba Buhari tun lokacin yayi kira ga yan Najeriya su zabi wanda suka ga dama a zaben 2023.”
Source:LegitHausa