Abubuwa da-dama sun faru a majalisar wakilan tarayya da ta dattawa a shekarar bara, wannan rahoto ya tattaro wasu daga cikin manyansu.
1. Sabani a kan dokar zabe
An yi ta kai-komo tsakanin majalisa da bangaren zartarwa a kan dokar zabe, inda ‘yan majalisa su ka dage a kan wajibincin amfani da tsarin kato bayan kato wajen fito da ‘dan takara.
A farkon shekara aka yi garambawul ga sashe na 84 da ya hana masu rike da mukamai shiga takara.
2. Zaben tsaida gwani Rahoto na Daily Trust ya ce mafi yawan ‘yan majalisa sun nemi tikiti domin su zarce a 2023, amma da yawa ba za su dawo ba, daga cikinsu har da shugaban majalisar dattawa, Dr. Ahmad Lawan.
3. Tsige shugaban kasa
Daga nan kuma sai aka ji ‘yan majalisa sun bada wa’adin makonni shida a kawo karshen rashin tsaro, idan ba haka ba suka ce za su tsige shugaban kasa, a karshe dai hakan bai yiwu ba.
4. Cushe a kundin kasafin kudi Jaridar
The Cable ta rahoto cewa a shekarar bara, zargin yin cushen biliyoyi a cikin kasafin kudin NUC, ma’aikatun tsaro, lantarki da na jin kai ya jawo surutu a zauren majalisar tarayya.
5. Tsarin mulkin kasa
Har ila yau, ‘yan majalisa sun yi kokarin yi wa tsarin mulkin kasa garambawul kamar yadda aka saba.
Amma ‘yan majalsar sun zargi Gwamnonin jihohi da hana ruwa gudu wajen aikin. Zaman karshe na Majalisar Tarayya a 2022.
6. Akawun majalisa A shekarar nan, an dauki tsawon lokaci ana rigima a kan kujerar Akawun majalisa tsakanin Sani Magaji Tambuwal da Amos Olatunde Ojo wanda ya kamata ya yi ritaya a farkon bana.
7. Majalisa da Gwamnan CBN Gwamnan babban banki ya ga ta kan sa a dalilin kawo dokar takaita kudi da canjin takardun Naira.
Wannan ya sa ‘yan majalisar kasar suka gayyaci Godwin Emefiele domin ya yi masu bayani.
Kudirorin da suka tada kura
8. Kudirin ruwa Rahotannin sun nuna a cikin kudirorin da suka jawo abin magana akwai kudirin albarkatun ruwa da Hon. Sada Soli ya dawo da shi.
A shekarar 2020, an yi fatali da wannan kudiri daga majalisar Najeriya.
9. Kudirin mata da shigan maza Hon. Muda Lawal ya kawo kudirin da zai haramta yin shiga ta kishiyar jinsi.
Daga baya an ki amincewa da kudirin domin akwai al’adar da aka san maza da daura zani ko makamantansu a wasu yankuna. 10. Kudirin da zai ba mata karfi
A 2022 aka kawo kudirin da ya nemi ya kara yawan kujerun mata a majalisa, ya kuma ware masu 20% a FEC da SEC tare da ba su damar zama ‘yan jihohin mazajensu, kudirin bai samu shiga ba.
Obasanjo a kan takarar Tinubu, Atiku, Kwankwaso
An ji labari, a matsayinsa na wanda ya yi aiki da duk manyan ‘yan takarar Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo ya bada ma’aunin da za ayi amfani da shi.
Obasanjo yana ganin a cikin Tinubu, Atiku da Kwankwaso, babu mai abin-a-nuna, manufofi, halayen kwarai da lafiyar da zai mulki Najeriya irin Peter Obi.