Abdoulaye Issa ya ziyarci Unguwar Makoko, daya daga cikin unguwannin da jama’a ke zama akan ruwa domin ganin yadda rayuwa take, kuma ga rahotan da ya hada mana.
A wani labarin na daban gwamnatin Jihar Lagos a tarayyar Najeriya ta fara rushe wasu matsugunai a cikin Jihar domin tsabtace birnin da kuma bude hanyar da za raya birnin kamar yadda hukumomi a Jihar su ka fada.Akalla mutane dari biyu ne mazauna anguwar da ake kira Makoko su ka rasa matsuguninsu sanadiyar rushe gidajensu.
Sai dai kungiyar nan mai fafutukar kare mahalli da ake kira Environmental Rights Action Friends of the (Earth ERA/FoEN), ta yi Allah wadai da wannan mataki da gwmanatin Jihar ta Legas ta dauka.
A cewar kungiyar a wata takardar da ta gabatarwa manema labarai,wanda kakin kungiyar, Philip Jakpor, ya saka hannu, rushe gidajen mazauna anguwar Makoko wanda mafi yanwansu masunta ne ya nuna cewa gwamnatin Jihar Legas bata san talakawa.
Ya kara da cewa wa’adin da aka ba wa mazauna anguwar na sa’oi 72 ya keta hakkin Bil Adama kana kundin tsarin mulkin Najeriya bai yadda da haka ba.
Takardar ta kara da cewa, batun za a yi amfani da wurin don a yi ginaginen zamani ya nuna cewa ba bu tunanin talakawa a zuciyar gwamnatin.
A ranar 12 ga watan Yuli, gwamnatin Jihar Legas ta aikewa da mazauna anguwar Makoko, da takarda wacce ke dauke da sa ka hanun, shugaban Kwamitin da ke yaki da rashin da’a a Jihar Legas, Mista Akin Tijjani, da su fice daga yankin a cikin sa’oi 72.
Takardar ta kuma umurci mutanen anguwar da su cire duk kayayyakin da su ka yi amfani da su wajen gina gidajensu.
Mafi yawan gidajen wadanda ke kan ruwa da je anguwar ta Makoko da katako aka gina su.
A cewar ERA/FoEN, wani mazaunin anguwar ta Makoko, Cif Mesu James Abraham, ya ce, babu inda za su je idan su ka bar wannan wuri ya kuma kara da cewa duk rayuwarsu anan ta ke.
“A yanzu haka babu inda zan je tare da iyalai na, inda san samu ne gwamnati ta mai da mu wani waje”. In ji Abraham.