Rahotanni masu karo da juna na nuna cewa sojojin Najeriya ne suka kashe shi, yayin da wasu majiyoyi kuma ke cewa a rikicin cikin gida ya mutu.
Ya zuwa wannan lokaci sojojin Najeriya basu sanar da kashe shugaban na kungiyar ISWAP ba.
Shidai Al-Barnawi ‘da ne ga Muhammadu Yusuf, mutumin da ya kafa kungiyar boko haram kafin jami’an tsaron Najeriya su kashe shi a shekarar 2009 lokacin da ya kaddamar da yaki akan su, abinda yayi sanadiyar mutuwar akalla mutane sama da dubu guda a lokacin.
A shekarar 2016 kungiyar ISWAP ta sanar da nada Al Barnawi a matsayin jagoran ta wanda kafin nan Abubakar Shekau ne ke jagoranci.
Kafin sauke Shekau daga jagorancin kungiyar ya bayyana goyan bayan sa ga kungiyar IS a watan Maris na shekarar 2015, tare da kashe dubban mutane sakamakon kai hare hare a garuruwa daban daban da jikkata mutane da kuma lalata kadarori daban daban.
Kawar da shi daga jagorancin kungiyar a shekarar 2016 ya bada damar nada Al Barnawi a matsayin sabon jagora da kuma raba mayakan kungiyar zuwa gida biyu.
Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya tace an nada Al Barnawi ya jagoranci kungiyar a Yankin Tafkin Chadi ne saboda hukunta Shekau wanda ya sabawa dokokin ta da kuma ci gaba da samun goyan bayan mayakan kungiyar da suke tare da manufofin mahaifin sa Muhammad Yusuf.
Jaridar tace rahotanni sun ce kungiyar ISIS ce ta horar da Al Barnawi kafin ya zama shugaban ISWAP, yayin da ya kaddamar da zafafan hare hare, ciki harda wadanda suke kaiwa sansanonin soji a Yankin Tafkin Chadi, yayin da ya kaddamar da manufofin kawar da tasirin Shekau.
Bayanai sun ce Al Barnawi ya mallaki yanki mai girma a arewacin jihar Borno, inda ya sanya haraji akan mazauna wurin, yake kuma tara kudi sosai daga aikin kamun kifi, bayan taimakon da yake samu daga kungiyar ISIS.
Rahotanni sun ce mayakan Al Barnawi sun lalata sansanonin soji da dama a Dikwa da Monguno da Abadam da kuma Marte dake Jihar Borno da kuma Geidam dake Jihar Yobe, tare da kafa sansani a Tafkin Chadi inda yake kai hari Najeriya da Nijar da Chadi