A tattaunawarsa da LEADADERHIP Hausa, wani babban dila a bangaren sayar da Raguna a gafen titin Unguwar Hayin Malam Bello a Kaduna, Ishak Aliyu Babayo ya ce; farashin raguna a bana, abin sai dai kawai addu’a. “Manyan muna sayar da su daga Naira 300,00 zuwa 350,000 a bana, wadanda a bara farashinsu, bai wuce daga Naira 150,000 zuwa sama ba, ya danganta da girmansa. Mun sayar wasu kananan a bara daga Naira 70,000 zuwa Naira 80,000, amma a bana farashin nasu ya yi matukar tashi.
“Hatta kudaden da muke jigilarsu zuwa cikin Kaduna daga jihohin da muke sayowa, ya rubanya, domin a bara muna jigilarsu a manyan motoci daga Naira 200,000 zuwa Naira 250,000, amma a bana muna biyan daga Naira 400,000 zuwa sama, ya danganta da nisan garin da muka sayo su,” in ji shi.
Har ila yau, “Farashin abincinsu ya karu; misali Kowar Farin Wake a bara ana sayar da ita kan Naira 3,500, amma a bana ta kai Naira 10,000 zuwa 11,500”.
Ya ci gaba da cewa, ana sayar da Kaikayin Dawa a bara kan Naira 2,500, amma a bana ya kai Naira 7,500, inda kuma buhun Dusa a bara ake sayar da shi kan Naira 5,000, a bana kuma ya kai Naira 7,500 ko sama da haka.
Binciken da wakilinmu ya yi a fitacciyar kasuwar nan ta sayar da dabbobi da ke Tudun Wada Kaduna, ya gano yadda ake samun karancin masu zuwa kasuwar, don sayen wadannan Raguna a bana.
Wani babban dila a ksuwar, Alhaji Kabir Sani ya danganta tashin farashin, musamman na Rugunan a kan kalubalen rashin tsaro, musamman a Jihar Zamfara; inda nan ne mafi akasari suke zuwa domin kawo dabbobin.
A cewarsa, akwai kuma manya wadanda duk guda daya ya kai daga Naira 800,000 zuwa Naira miliyan 1.4, wanda farashin daya a bara, bai wuce Naira 500,000 ba, duk da cewa ko shakka babu; wannan na da alaka da tashin farashin kayan masarufi da kuma matsin tattalin arziki da ake fama da shi a wannan kasa.
DUBA NAN: Matakan Da Gwamnatin Kano Ta Dauka Dangane Da Ilimi
Haka nan, a Kasuwar Kawo; wani dilan sayar da Raguna a gefen hanyar titin Waff duk dai a Kadunan, Awwal Mohammed ya ce; farashin Rago daya da ake sayarwa kan Naira 200,00 a bara, bana ya kai Naira 400,000, matsakaici kuma a bana ya kai Naira 300,000, inda muke sayar dan karami kuma a kan kudi daga Naira 100,000 zuwa Naira 150,000 ko sama da haka, ya danganta da girma Ragon.